An kashe manoma uku a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a cewar majiyoyi a yankin.
- Ambaliyar Ruwa: Mutum 1 Ya Mutu, An Ceto 4 A Abuja
- Za Mu Dawo Da Martabar ‘Yansanda A Idon ‘Yan Nijeriya -Sufeton ‘Yansanda
Usman Kasai, shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) ya tabbatar da faruwar harin.
Ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa na aiki ne a gonakinsu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari.
Wadanda aka kashen sun hada da Anas Sabonlayi, Abubakar Dankibiya, da Harisu Un-Guwar Lemu.
Sun kasance mazauna Sabon Layi, karkashin Unguwar Kakangi.
Ana kara nuna damuwa kan karin hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a yankin.
Idan ba a manta ba a makonnin da suka gabata, al’ummar yankin sun sha fuskantar irin wannan harin wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen kauyen tara tare da tilastawa wasu da dama barin gonakinsu.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin jihar ko hukumar ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ce yana tsaka da wani taro.
Amma ya yi alkawarin kiran wakilinmu, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kira ba.