Wasu rahotanni da ke fitowa daga Jihar Gombe, sun bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan Sheikh Ibrahim H. Musa, wanda aka fi sani da Albanin Kuri tare sa hallaka shi.
Leadership Hausa ta samu tabbacin labarin ta hanyar wani sako da shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Bala Lau ya wallafa a shafinsa na Facebook.
- Shugabar NIS Ta Ziyarci Jami’an Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Sakkwato
- Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Zanga-zangar Da Suka Shirya
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.!
“Barayi sun haura cikin gida sun kashe mana daya daga cikin malamanmu, Sheikh Ibrahim H. Musa Albanin Kuri cikin daren Larabar nan.
“Za a gabatar masa da jana’iza da misalin karfe 1 na rana a masallacin JIBWIS na Bolari Gombe in sha Allah.
“Ku saka mana shi cikin addu’oinku, Allah Ya masa rahama.”
Tuni al’ummar Musulmi daga cikin gida Nijeriya da wajenta suka shiga aike sakon ta’aziyyarsu kan rasuwar shehun malamin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp