Hukumomi a birnin Beijing, sun ce an tabbatar da mutuwar mutane 33 sakamakon wata ambaliyar ruwa a babban birnin China ya fuskanta a makon da ya wuce.
Hukumomin sun ce har yanzu ana neman wasu mutane 18 da ba a san inda suka shige ba.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sheikh Albanin Kuri A Gombe
- Shugabar NIS Ta Ziyarci Jami’an Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Sakkwato
Guguwar dai ta daidaita birnin Beijing, inda ta dangana da lalata Arewa Maso Gabashin gundumar Jilin.
Gwamnatin China ta girke dubban sojoji da jamai’an sa kai a Jilin, daidai lokacin da ake sa ran guguwar Doksuri na gab da isa can, tuni kuma aka kwashe dubban mutanen da ke zaune a yankin.
Wannan dai ba shi ne karon farko da irin wannan ambaliya ta afku a yankin ba.
Sai dai gwamnati na ci gaba da daukar matakai don hana salwantar rayuka da duniyoyin jama’ar gundumar.