Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kone ofishin ‘yansanda na Umunze da ke karamar hukumar Orumba ta Kudu a Jihar Anambra.
Har wa yau sun kashe jami’an ‘yansanda biyu da ke bakin aiki a ofishin.
- Ambaliya: Atiku Ya Bai Wa Jihar Borno Gudummawar Miliyan 100
- Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Zayarci Maiduguri, Ta Yi Alƙawarin Ƙarin Tallafi
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari ne a ofishin ‘yansandan tare da amfani da ababen fashewa.
Sun yi ta harbe-harbe, yayin da wani bangare na ofishin ya kama da wuta.
An ruwaito cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar jami’an ‘yansanda biyu da ke bakin aiki a lokacin da suka yi kokarin kare ofishin.
Kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Amma ya ce an gano gawawwakin ‘yansandan da suka rasu, kuma an garzaya da su asibiti.
Ya kuma kara da cewa sun gano wasu abaubuwan fashewa guda biyar da ba su tashi ba, kuma suna bin sahun maharan domin kama su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp