Akalla kimanin dalibai 10 ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta samu rahotannin farko daga hukumomin tsaro kan sace dalibai 10 da aka yi a karamar hukumar ta Kachia.
- ‘Yan Siyasa Ne ke Kokarin Raba Kan ‘Yan Nijeriya —Solomon Dalong
- Gwamnatin Kano Ta Nada Jega A Matsayin Shugaban Jami’ar Sa’adatu Rimi
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
A cewar rahotannin farko, an yi garkuwa da daliban makarantar Sakandaren Gwamnatin Awon a ranar Litinin.
Ya ce har yanzu ba a tantance ainihin inda lamarin ya faru ba, inda ya kara da cewa ana jiran cikakkun bayanai don tantance ko lamarin ya faru ne a harabar makarantar ko kuma a wani wuri daban.
Kwamishinan ya yi alkawarin fitar da sanarwar ga jama’a da zarar an samu karin bayani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp