Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani ma’aikacin hukumar babban birnin tarayya Abuja tare da wasu akalla mutane 15 a rukunin gidaje 1,000 da ke Pegi a karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja ranar Lahadi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe, sannan suka yi awon gaba da mutanen da suke komawa gida daga aiki.
- Inter Milan Ta Je Wasan Karshe Na Gasar Zakarun Turai
- Kasar Sin Da Kasashe Biyar Na Tsakiyar Asiya Sun Bude Sabon Babi Na Sada Zumunta Tsakaninsu
Shugaban kungiyar mazauna garin Pegi Taiwo Aderibigbe ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya kara da cewa daga cikin wadanda aka sace har da ma’aikatan sashen kula da ci gaban babban birnin tarayya Abuja a karkashin hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja.
Aderibigbe ya ce, “’Yan bindiga sun sace mutane 15 a kan titin Pegi mai nisan kilomita 14, kuma daga cikin wadanda aka sace akwai Shu’aibu Musa, ma’aikacin FCTA.
“Mun kuma lura cewa mijin matar da ke sayar da kayan sawa a babbar kofar shiga gidan yana cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke dawowa daga aiki.
“Masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba a halin yanzu, amma har yanzu muna kokarin gano wasu mazauna garin da aka sace.”
Kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta amsa tambayoyi kan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, duk da kiran waya da sakon kar ta kwana da aka aike mata.