Aƙalla mutum shida ne suka rasa rayukansu yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Marit da Gashish da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato, a ranar Litinin.
Shaidu sun ce maharan sun zo ne ba tare da wani gargaɗi ba, suka fara harbe-harbe, inda suka kashe mutane tare da jikkata wasu da dama.
- Zulum Ya Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira 6,000 Garuruwansu A Borno
- Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini
Shugaban ƙaramar hukumar Barkin Ladi, Hon. Stephen Gyang, ya tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’ar yaɗa labaran hukumar, Mercy Yop Chuwang.
Gyang ya bayyana harin a matsayin abin takaici, musamman a lokacin da ake ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a yankin.
Ya ziyarci waɗanda suka jikkata a Asibitin Gwamnati na Barkin Ladi, inda ya nuna alhini da baƙin ciki harin.
Ya gode wa jami’an tsaro da ‘yan banga bisa ƙoƙarinsu, amma ya buƙaci su ƙara ƙaimi don hana faruwar irin haka a gaba.
Shugaban ya kuma buƙaci shugabannin al’umma, jami’an tsaro da mazauna yankin su haɗa hannu don kawo ƙarshen rikicin da tabbatar da zaman lafiya.
Gyang ya roƙi Allah Ya bai wa iyalan waɗanda suka rasu haƙuri rashin su, tare da umartar ma’aikatan lafiya su gaggauta bai wa wadanda suka jikkata kulawar gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp