Wasu ‘yan bindiga da suka kai harin bam a ofishin ‘yansanda na Ogidi da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra, sun kashe ‘yansanda uku.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar.
- An Gurfanar Da Sojoji 68 A Gaban Kotu Kan Zargin Rashin Da’a A Sokoto
- Ilimin Taurari Zai Iya Warware Matsalolin Da Kasar Nan Ke Fuskanta –Shaikh Muhajjadina
Majiyoyi a yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun far wa ofishin ‘yansandan inda suka dinga harbi ko ina sannan suka jefa bama-bamai cikin ofishin inda suka kone ginin.
Kakakin ‘yansandan Jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an tura tawagar ‘yansanda domin dawo da tsaro a yankin.
Ya ce, “Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta kara karfafa tsaro a yankin Idemili na Arewa da ke jihar, biyo bayan harin da aka kai wa rundunar ‘yansandan yankin Ogidi da sanyin safiyar yau, inda ‘yansanda uku suka rasa rayukansu.
“Yan bindigar sun fara harbe-harbe kan rundunar ‘yansandan, sannan sun jefa bama-bamai.
DSP Tochukwu ya kara da cewa baya ga ‘yansandan uku da aka kashe, an kone ofishin ‘yansandan.
Ya kara da cewa: “Rundunar ta damu da asarar rayuka da dukiya sakamakon wannan harin.”
Ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali tare da tabbatar da cewa kwamishinan ‘yansanda, CP Echeng Echeng, ya jajirce wajen hana wadannan miyagu ci gaba da kai hare-hare.
Ya bayyana cewa, CP Echeng ya kara daukar matakai na inganta tsaro da rayuka da dukiyoyi a jihar, inda ya ce tuni aka fara tantance harin da aka kai ofishin ‘yansanda na Ogidi.