‘Yan Sanda shida da suka fafata da ‘yan Bindiga da suka kai wa ayarin motar da ke dauke da Maniyyatan jihar Sakkwato sun rasa rayukansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an kai wa motar harin ne a dajin Gundumi lokacin da ayarin ke kan hanyarsu ta zuwa filin Jirgin sama na garin Sakkwato domin jigilar Maniyyata zuwa kasa mai tsarki.
An ruwaito cewa, daukacin Maniyyatan an kubutar da su inda aka maido su zuwa Fadar Sarkin Gobir Isa ba tare da dayansu ya samu wani rauni ba.
Sai dai, wani mazaunin garin na Isa da ya bukaci a ba ya sakaya sunansa ya shedawa jaridar Daily Trust cewa, ‘yan Bindigar sun hallaka ‘yan sanda shida
Ya kara da cewa, ‘yan Bindigar sun yi wa motar kwanton Bauna ne wacce ‘yan sandan suka yiwa rakiya, ‘yan sandan sun yi musayar wuta da ‘yan Bindigar hakan ya taimaka motar da ke dauke da Maniyyatan ta samu kubuta.
Kakakin yada labarai na Gwamnan Jihar Muhammad Bello wanda ya tabbatar da kai harin a cikin sanarwar da ya fitar ya ce, Jami’an Gwamnatin jihar ne suka karbi Maniyyatan.
Da aka tuntubi mai rikon kwarya na kakakin yada labarai na rundunar ‘yan Sanda na jihar ASP Ahmad Rufa’i, ya bayyana cewa ba a yi masa bayani a hukunce kan mutuwar abokan aikin na sa ba.