‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani dan takarar kansila mai suna Japheth Zarma Yakubu a unguwar Kurmin-Kare da ke karamar hukumar Kachia a Jihar Kaduna, na neman a biya su kudin fansa Naira miliyan 20 da babura biyu.
Wani shugaban al’umma ne, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce shugaban ‘yan bindigar ya kira a ranar Lahadi da misalin karfe 11:45 na safe ta wayar wanda lamarin ya shafa, inda ya bukaci ‘yan uwansa su tara musu Naira miliyan 20 da babura biyu.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Shaida Cewa Ba Lallai Ba Ne A Ci Nasara Daga Faduwar Wani Bangare Ba
- Gwamna Uba Sani Zai Kaddamar Da Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ungozoma A Pambegua
Ya ce daya daga cikin ‘yan uwan wanda aka sace yana tattaunawa da maharan kan kudin fansar.
Ya kara da cewa, “A safiyar yau ne dan uwan wanda aka sace ya zo wajena ya sanar da ni yadda ya yi magana da shugaban ‘yan bindigar.”
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba a samu damar jin ta bakinsa ba kan lamarin.
Idan za a tuna cewa Leadership ta ruwaito cewa ‘yan bindigar, a ranar Alhamis din da ta gabata, sun yi garkuwa da dan takarar a lokacin da ya je duba gonarsa.