Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

BABBAN LABARI: ‘Yan Biyafara Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne –Gwamnatin Amurka

by Tayo Adelaja
September 25, 2017
in MANYAN LABARAI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Gwamnatin Amurka a karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta ce ba ta kallon kungiyar ’yan kabilar Igbo masu rajin neman ballewa daga Nijeriya (IPOB) a matsayin ’yan ta’adda, wanda hakan ya saba da ra’ayin gwamnatin tarayyar Nijeriya.

samndaads

Wannan kalami ya fito daga bakin mai Magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ne, Russell Brooks, lokacin da ya ke mayar da martani kan tambayar da a ka yi ma sa a kan ra’ayin Amurka kan matsayin IPOB da alaka da ta’addanci a karshen mako.

Gwamnatin Shugaba Trump na Amurka ta kara da cewa, duk da cewa ta na da muradin ganin an warware rikicin da ke tsakanin ’yan IPOB cikin masalaha, sabanin matakin da mabiya kungiyar su ka dauka na haike wa Hausawa mazauna yankin nasu na Kudu maso gabashin Nijeriya, amma duk da haka kungiyar IPOB ba ta dace da yadda dokokin Amurka su ka wassafa ta’addanci. Don haka Amurka ba za ta iya ayyana IPOB a matsayin ’yar ta’adda ba a yanzu gaba-gadi.

“Don haka Amurka ta na goyon kasancewar Nijeriya a dunkule, sabanin abinda ’yan kungiyar Biyafara ke nema, amma saidai kungiyar ba ta gama cika sharuddan zama ’yan ta’adda ba a idanun Amurka.”

Idan dai za a iya tunawa daraktan yada labarai na rundunar sojin Nijeriya, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana ’yan Biyafaran a matsayin ’yan ta’adda bayan da su yi arangama da dakarun sojoji a garin Umu’ahia babban birnin jihar Abia lokacin da su ke kokarin ceto Hausawan da ’yan kungiyar su ke yiwa kofar rago.

A yayin da Manjo Janar Enenche ya ke bayyana dalilan da rundunar sojin ta dogara da su wajen yanke wannan hukunci ya ce, mambobin kungiyar sun yi amfani da “duwatsu, kwalabe, adduna da sauran makamai kan sojojin da ke bakin aiki a ranar 10 ga Satumba, 2017.”

Bugu da kari, gwamnoni yankin na Kudu maso Gabas su ma sun fito karara sun yi tir da ayyukan kungiyar ta IPOB su na masu nesanta kansu da ita.

Jim kadan bayan hakan ne, gwamnatin tarayya ta shigar da kara gaban kotun tarayya da ke Abuja ta hannun antoni janar kuma ministan shari’a na tarayya, Malami Shehu, SAN, inda ta roki kotun da gaggauta ayyana ’yan Biyafaran a matsayin ’yan ta’adda, domin karfafa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bayar na haramta ayyukan kungiyar da kuma saka ta a jerin kungiyoyin ta’addanci a cikin kasar.

Gwamnatin tarayya ta jadda cewa, ya isa dalili kan yadda ’yan Biyafara su ka buga takardun kudinsu kuma su ke amsar kudi daga hannun mutane ’yan asalin yankin ta hanyar tilastawa, baya ga kuma yadda su ke yiwa mata da kananan yara fyade babu ji babu gani.

Sannan kuma su ke shigo da muggan makamai cikin kasar da nufin kasha rayukan bil adama. Don haka babu wani ta’addanci day a wuce wannan, domin idan ba a tsayar da su ba, ba a san irin ta’addanci da barnar da za su yi a gaba ba.

To, sai dai kuma ita ma IPOB ba ta yi kasa a gwiwa ba, inda ta garzaya kotun daukaka kara ta na mai kalubalantar hukuncin kotun, ta na mai cewa, an tauye ma ta hakkin da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba ta na ’yancin yin kungiyoyi, taruka da fadin albarkacin baki.

A yanzu haka dai a na gaban kotu, kuma gwamnatin tarayya ta kafe a kan bakanta, inda ma ta ke shirin daukar matakan katse hanyoyin kudaden shiga daga kasashen waje na haramtacciyar kungiyar.

Abin da ba a tabbatar ba har kawo hada wannan rahoton shi ne, ko gwamnatin Nijeriya ta fara neman hadin kan Amurka, domin a hada hannu a gurgunta ’yan Biyafaran. Haka nan kuma duk wani yunkuri na jin ta bakin gwamnatin tarayya kan wannan matsaya ta ofishin jakadancin Amurka ya ci tura.

SendShareTweetShare
Previous Post

An Fara Yunkurin Sasanta Kwankwaso Da Ganduje

Next Post

Saura Kiris!

RelatedPosts

Bude Makarantu

Korona: Ba Ja Baya Ga Bude Makarantu – Gwamnatin Bauchi

by Muhammad
4 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi ta...

Harshen Hausa

Taron ‘Waiwaye Adon Tafiya’: Masana Sun Damu Bisa Nakasta Harshen Hausa

by Muhammad
5 days ago
0

Akwai Damuwa Kan Yadda Zamani Ke Tafiya Da Al’adun Bahaushe...

'Yan Kwaya

Zaben Kananan Hukumomin Kano: Yadda Aka Tono ’Yan Kwaya A ’Yan Takara

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta...

Next Post

Saura Kiris!

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version