‘Yan Jarida Basa Yi Min Adalci, Cewar Zidane

Zidane

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta  Real Madrid, Zinedine Zidane ya bukaci ‘yan jarida su rika “mutunta” shi kuma ya ce har yanzu kungiyar tana fafatawa a gasar La Liga kuma zasu ci gaba da samun nasara.

Real Madrid tana mataki na uku a teburin gasar La liga, inda take bayan kungiyar Atletico Madrid, wadda ke saman teburin da maki 10 kuma duk da haka Real Madrid ta fi ta yawan buga wasa sannan yadda kungiyar ta gaza yin katabus a ‘yan kwanakin nan ya sa kafafen watsa labari sun soma caccakar Zidane, dan kasar Faransa.

“Abin da yake ba ni dariya shi ne yadda kuke tambaya ta me ya sa nake fushi bai kamata ‘yan jarida ku rika yi min abin da kuke yi min ba mun dauki kofi a kakar wasan da ta wuce domin haka ina ganin ya kamata ku mutunta ni” in ji Zidane a taron manema labarai ranar Juma’a.

Ya ci gaba da cewa “Mun samu damar fafatawa a gasar La Liga a kakar wasan bana, akalla hakan ya sa muna cikin kakar wasa sannan a kakar wasa mai zuwa, akwai bukatar sauyi, amma a wannan shekarar ku bar mu, tawagar da ta dauki kofi a kakar wasan da ta gabata tana fafatawa a kakar wasa ta wannan shekarar ai”

Ya kara da cewa “Ba wai mun shekara 10 ba ne (da daukar kofi), a kakar wasan da ta wuce ne kuma akalla ya kamata ku mutunta mu kan abubuwan da muka samu nasara a kansu ku (‘yan jarida) kun cika surutu sannan me ya sa ba za ku kalle ni ido da ido ku gaya min cewa kuna so a kore ni daga kungiyar nan ba, ba a bayan idona ba.”

An sake nada Zidane a matsayin kocin Real Madrid a watan Maris na shekarar 2019, bayan ya jagoranci kungiyar wajen daukar kofin Zakarun Turai sau uku a jere da kuma kofin lig a kakar wasa ta shekarar 2016 zuwa 2017 lokacin shugabancinsa na farko.

Dan kasar Faransa mai shekara 48 a duniya zai jagoranci kungiyar a fafatawa da kungiyar da ke kasan teburin gasar La Liga Huesca bayan Real Madrid ta sha kashi a hannu Lebante koda yake bai halarci wasan ba saboda ya kamu da cutar korona

“An killace ni tsawon mako biyu, na matsu na fito na kuma nuna wa duniya cewa zan jajirce har zuwa karshe kuma yanzu na dawo domin ci gaba da jagorantar wannan kungiya zuwa ga nasara kamar yadda na saba a baya,” in ji shi.

Sergio Ramos bai fafata ba a wasan da kungiyar ta buga saboda raunin da ya ji, a yayin da Zidane ya sanya masu tsaron raga uku a tawagarsa mai mutum 17 kuma ‘yan wasa Eden Hazard da  Dani Carbvajal da Federico Valverde da Rodrygo da Lucas Bazquez su ma ba su shiga karawar ba saboda jinya, yayin da aka dakatar da Eder Militao.

Exit mobile version