Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa (SSG), Barista Labaran Shuaibu Magaji, ya jaddada cewa ‘yan jarida na da muhimmiyar rawa wajen haɗa kan al’umma da gwamnati ta hanyar aikinsu na watsa labarai.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar ‘yan jarida reshen Jihar Nasarawa, yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a Lafia ranar Laraba.
- ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
- Babu Matsalar Da Za A Fuskanta Idan Majalisa Ta Tsige Fubara – Wike
A cewarsa, aikin jarida na wayar da kan al’umma, ilimantarwa da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Ya ce tun daga lokacin da ya karɓi muƙamin Sakataren Gwamnati, bai taɓa barin wata takarda ta wuce sama da awa biyu a teburinsa ba tare da aikawa inda ta dace ba.
Ya kuma tabbatar da cewa zai yi amfani da kafafen watsa labarai domin sanar da jama’a manufofin gwamnati da shirye-shiryenta.
Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule.
Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar.
Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su, domin tabbatar da sahihanci da ingancin aikin jarida.
Da yake ƙarin bayani, ya ce gwamnatin Abdullahi Sule ta kawo sauye-sauye masu amfani, musamman wajen inganta harkar haƙar ma’adinai a jihar.
Ya bayyana cewa Jihar Nasarawa ce ke kan gaba a Naieriya wajen samar da ma’adinan Lithium, wanda ke amfani ga ci gaban tattalin arziƙi.
A nasa jawabin, Shugaban ‘Yan Jarida na Jihar, Kwamared Isaac Ukpoju, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya sabon Sakataren Gwamnatin Jihar murna bisa naɗin da aka yi masa.
Ya ce naɗin da aka yi wa Labaran Shuaibu Magaji ya dace da shi, kuma ‘yan jarida ba su yi mamaki ba duba da irin tarihin ayyukansa.
Haka kuma, ya roƙi Sakataren Gwamnatin da ya haɗa su cikin harkokin yaɗa labarai na gwamnati, musamman a ɓangaren tallafa wa ayyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp