A ranar Talata ne wasu mutane wadanda ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne, sun tarwatsa harkokin karatu a makarantar sakandare ta Oba Akenzua da kuma kwalejin Ihogbe da ke Benin Jihar Edo. Nan take jami’an ‘yan sanda suka isa wurin, hakan ya ceci rayukan mutane, inda dalibai da dama suka samu raunika wanda maharan suka yi musu da wuka da kuma adduna. Dukkan makarantun suna kallon juna, inda suke kan titi ICE Road kusa da hanyar Wire cikin garin Benin.
Wadanda lamarin ya auku a gaban idanunsu sun bayyana cewa, malamai da dalibai sun gudu wurare daban-daban lokacin da ‘yan kungiyar asirin suka fara harbe-harbe tare da farmakar dalibai. An bayyana cewa, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asirin sun labe a yankin suna dakon wasu dalibai wadanda ake zargin yaran ‘yan kungiyar asiri ne wadanda suke hamayya da juna, inda suka fara jifan su da duwatsu.
Bayan haka, ‘yan kungiyar asirin sun fara farmakin duk dalibi da suka gani. An bayyana cewa, daya daga cikin daliban ya samu mummunar rauni inda aka garzaya da shi zuwa asibiti.
Jami’an tsaro masu yawa sun isa makarantar lokacin da wakilinmu ya ziyarci wurin da lamarin ya auku. Wakilinmu ya lura da maharan guda biyu wadanda ‘yan sanda suka cafke, suna ta kuka tare da fadin cewa su ba masu laifi ba ne. Mazauna yankin sun bayyana cewa, farmakin ‘yan kungiyar asiri yana kara karuwa a cikin ‘yan kwanakin nan a yankin.
Kwamishinan ilimin Jihar Edo, Emmanuel Agbale, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa babu wani dalibi da ya rasa ransa a cikin wannan farmakin. Agbale ya ce, lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin, nan take ‘yan kungiyar asirin suka gudu. “Ko da yaushe daliban makarantun suna fada da junan su. Jami’an tsaron za su kasance a yankin. Za a gudanar da tare-tsare a dukkan makarantun. A halin yanzu, an rufe makarantun sakamakon wannan farmakin,” in ji kwamishina.