Daga Rabiu Ali Indabawa
Shugaban rikon kwarya mai kula da shirin ofishin Amnesty International na fadar shugaban kasa (PAP), Kanal Milland Dikio ya bayyana cewa ‘yan kwangila na bin ofishin Amenesty International Naira biliyan 71.4b. Dikio ya ce adadin wanda kwamitin bincike ya kawo, ya fi na kasafin kudin shekara-shekara na PAP.
Amma, ya bayyana cewa biyan ‘yan kwangilar zai kasance ne bisa ka’idojin da yarjejeniyar ta kulla da su. Da yake magana a wani shirin talabijin kai tsaye a jiyak , Dikio ya kuma bayyana cewa wasu masu cin gajiyar PAP na iya samun horo na kare bututun mai domin basu damar samun karin kudi.
Ya ce: “Kwamitin binciken ya tabbatar da cewa ‘yan kwangila na bin kusan Naira biliyan 71.4, kuma hakan ya fi kasafinmu na shekara na Naira biliyan 65. A namu bangaren, abin da muka dukufa wajen yi shi ne tabbatar da an yi amfani da hankali wajen samar da kudade a cikin lamuran da ake bukata.
Ya kara da cewa, ya kuduri aniyar cimma burin shirin daidai da matsayin da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya. Shugaban na Amnesty, wanda ya ce ba za a taba nada wani manajan shirin ba a lokacin da Majalisar Dinkin Duniya za ta yi wannan shirin, ya lura cewa da wasu kwararrun ma’aikata, PAP za ta cimma burinta a cikin lokaci.
Kalaman nasa: “Ina tattaunawa da yadda Majalisar Dinkin Duniya take gudanar da ayyukanta na DDR. Ofishin Amnesty ya zama wani wurin ganawa na haya. Wannan ya yi nesa da yadda a ke gudanar da shiri kamar wannan.
“Na yi niyyar sake tsara wurin tare da albarkar shugabanni don kirkirar da injina masu inganci da walwala ta yadda za mu iya sarrafa kowane bangare na shirin tare da samun kwararrun ma’aikata, yadda za mu iya isar da tsari a kan lokaci.
“Aikina ya yanke mi ni. Lokacin da a ka nada ni kuma na ci gaba a ranar 21 ga Satumba, kwamitin bincike ya yi bincike mai yawa game da abin da ya faru kuma ina ganin ba za mu zauna a kan abubuwan da su ka gabata ba. Amma, idan mu ka koyi darussan da suka gabata, za mu yi kyau.”
Dikio ya ce ya shirya tsara ayyukan ofishin na Amnesty ne da kuma nuna yadda za a rage cin hanci da rashawa. “Akwai korafe-korafe da yawa da nake ganin an aiwatar da su. Misali, muna son dijital ayyukanmu da kirkirar tsarin da za’a samu mu’amala a bayyane. Idan muka yi haka da kyau, zai rage abubuwan da ke faruwa na cin hanci da rashawa,” in ji shi.
Game da korafin rashin biyan wasu alawus-alawus, ya ce ofishin na Amnesty zai biya ne kawai don amfanin da aka samu a cikin littattafan. Ya ce an biya kudaden makaranta da sauran alawus na galibin wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu a karaashin shirin, ya kara da cewa ana shawo kan matsalar da ta shafi dalibai 1,880.
Dikio ya ce: “Ina son sanar da gaskiyar cewa akwai wasu korafe-korafe na alawus din da ba sa cikin littattafan. Yanzu, ba mu da alhakin biyan abubuwan da ba sa cikin littattafan. Amma, idan suna bayyane a cikin littattafan, za mu tabbatar da cewa masu cin gajiyar sun karbi abin da ya dace da su.
“A na tsakiyar aikin yadda za’a warware wannan lamarin, sai batun #EndSARs ya taso. Don haka, na ba da shawarar cewa duk daliban da za a tabbatar da su ya kamata su yi abin da a ke bukata game da tantance asalinsu. Na isar da sako cewa za su iya zuwa kotu don rantsuwa da takaddar rantsuwa cewa su ne su ne daliban Bonafide ne na jami’o’in da su ke da’awa.
“Su dauki takardun rantsuwa zuwa shugabannin sassansu ko shugabansu na kwarai. Dukkan abin da ya kanasce an tura da shi in da ya dace an kammala. Na kasance cikin rangadi na kwanaki 13 yanzu kuma idan na koma, zan duba jerin amincewa da biya kuma za mu magance hakan. Za mu tabbatar a lokacin da ya dace idan wadancan abubuwan da aka gabatar gaskiya ne.
“Aiki ne mai wahala, amma muna da kwarin gwiwa tare da hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki, hukumomin gwamnatin tarayya da makamantansu za mu cimma wannan burin”.
Dikio ya ce ofishinsa ya himmatu wajen inganta kunshin wadanda ke cin gajiyar shirin, inda ya kara da cewa ya tuntubi karamin Ministan Man Fetur, Cif Timipre Sylba, kan yadda wasu daga cikinsu za su shiga aikin horar da bututun mai.
Ya ce: “Idan mu ka yi kwalliya mai kyau muka fitar da su cikin ‘yan kasuwa masu zaman kansu, za su kasance a cikin matsayin da suke samun sama da 65,000 kuma maimakon haka su zama masu daukar ma’aikata kwadago.
“A gaskiya, karamin Ministan Man Fetur ya lasa mana zuma a baki kuma mun gabatar da hakan. Mu na son hada hannu da Ma’aikatar Man Fetur don tura wasu daga cikin wadanda muka horar zuwa shirye-shiryen kare bututun mai.
“Hakan zai ba su damar samun karin kudi sama da Naira 65,000. Ba ma so mu bar mutane masu dogaro da alawus-alawus.”