Tun ranar Juma’a da ta gabata da Allah ya karbi ran Hakimin Madobi kuma Makaman a Masarautar Karaye, Alhaji Musa Sale Kwankwaso, wanda kuma mahaifi ne ga tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, jama’a, manya, shugabanni da ’yan kasuwa, malamai da sarakuna, jami’an gwamnati da sauran al’umma daga ko’ina cikin Nijeriya har da makota ke tururuwa zuwa ta’a ziyya da jajenta wa Madugun na Kwankwasiyya.
Sai dai ziyarar da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, dan Majalisar Wakilai a Majalisar Tarayya ta Abuja daga karamar hukumar Birnin Kano a jam’iyar APC kuma makusanci na hannun daman Shugaban Kasa Muhammad Buhari ziyarar ta’aziyar ta Sharada ta dauki hankalin duniya kan irin gagarumar tarba da mabiya Kwankwasiyya karkashin Sanata Kwankwaso su ka yi ma sa duka da kasancewarsa dan jam’iyyar APC a wannan lokaci.
Shi ma a jawabinsa Hon Sha’aban Ibrahim Sharada ya nuna farin cikinsa da irin tarbar da a ka yi ma sa a gidan Sanata Kwankwaso da ke Milla Road, inda a ke zamam makokin na Makaman Karaye da ya rasu, inda Sha’aban ya nuna gamsuwasa da akidar cigaba irin ta Madugun Kwankwasiyya da mabiyansa na yin adalci ga kowa da siyasa bada gaba ba.
Tuni dai Mataimakin Gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna, da wazirin Masarautar Gaya Dattijo kuma sakataran Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji su ka jagoranci wani ayari na jami’an Gwamnatin Kano dan ziyarar ta’a ziya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan rashin da akayi masa a wanan lokaci a madadin Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje haka shi ma mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayaro SAN KANO inda kuma su kayi adu’a ta Neman rahama da gafara ga Marigayi da kuma ba Sanata Rabi’u hakuri da sauran iyalan kan rashin makaman karaye wanda ya kwanta dama a Ranar Juma’a da ta gabata.