A kokarin tsaftace harkokin zabe a Nijeriya, ‘yan majalisar wakilai sun gabatar da kuduri na samar da hukunci mai tsanani ga masu karya dokar zabe.
A ranar 23 ga watan Agustan 2023, ‘yan majalisar wakilai sun gudanar da zaman jin ra’ayoyin jama’a, domin samun amincewar masu ruwa da tsaki na neman samar da hukunci mai tsanani ga masu karya dokar zabe.
- Mace Za Ta Iya Yin Limancin Sallah?
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
Rikici na daya daga cikin abubuwan da ke damun zaben kasar nan wanda ke tarwatsa lamura gabanin zabe da kuma bayan gudanar da zabe.
Dalilan da suke haddasa rikici shi ne bambanci. Irin wadannan laifuka ana amfani da su a wajen abokan takara ko wajen yin mugudi a lokacin zabe.
‘Yan siyasa suna biyan wakilansu wajen yin kalamun batanci ko daukan nauyin ‘yan daba domin farmakar runfar zabe ko sace akwati ko lalata takardun zabe ko sayan kuri’u ko yin garkuwa ko kashe abokan takara da magoya bayansu.
Tun kafin babban zaben 2023, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fara fadakarwa.
Amma abun takaicin shi ne, a cikin dokar zaben da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a watannin da suka gabata ta kasa samar da tsauraren hukunci da za a yi wa wadanda suka karya dokar zabe.
Domin kawo karshen rikicin zabe, ‘yan majalisa sun samar da kudurin dokar hukunta masu karya dokar zabe wanda ya tsallake karatu na farko da na biyu, inda har ya kai da sauraron jin ra’ayoyin jama’a a kan kudurin.
A wurin zaman jin ra’ayoyin jama’a, Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya nuna goyon bayansa ga kudurin, wanda ya bayyana cewa lokacin da kudurin ya zama doka, hukumarsa za ta samu kunciyar hankali na tabbatar da an hukunta wadanda suka karya dokar zabe, musamman muyagun ‘yan siyasa masu daukar nauyin ‘yan daba wajen tayar da zaune-tsaye.
A cewarsa, sake fasalin harkokin zabe ba zai yuwu ba har sai an hukunta wadanda suke karya dokar zabe.
Yakubu ya kara da cewa hukumar INEC tana da nauyi masu yawa da suka rataya a wuyanta ciki har da gurfanar da masu karya dokar zabe duk da irin kalubalen da hukumar ke fuskanta.
Ya ce tun daga zaben 2015, sun samu laifuka guda 125 game da karya dokar zabe a kotuna mabambanta, amma masu laifi 60 aka iya hukuntawa.
Tun da farko da yake gabatar da kudurin a zauren majalisa, shugaban majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa rikicin zabe yana janyo karancin inganci da cin hanci da rashawa da rikicin shugabanci, wanda suke taimakawa wajen magudin zabe ta yadda masu laifi suke iya juya gwamnati sabani tsarin dimokuradiyya.
Gbajabiamila wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Hon. Idris Wase ya ce ko shakka babu akwai bukatar yin aiki sosai wajen tsaftace kasar nan daga rikicin zabe da karya dokar zabe.
Kudurin dokar na shafi 19 ya tanadi hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari ga duk wanda aka samu da tsoma baki da taka rawa wajen bayar da rashawa kan zabe.
Sanna sashe na 26 ya tanadi hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari ko tarar naira 40,000, 000 ga duk wanda aka kama da kwacewa ko lalata takardun zabe ko kuma duk wani kundi da ya shafi zabe.
Haka ma sashi na 32 na kudurin dokar ya tanadi hukuncin daurin shekaru 10 ko tarar naira miliyan 40 ga masu kalammun batanci a kan zabe.
Hakazalika, kudurin dokar na shafi 13 ya tanadi hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari ko tarar naira 3,000,000 ga duk wanda aka samu da magudin zabe ko bayar da jawaban karya lokacin da INEC take bayar da katin zabe.
Sannan sashi na 25 ya tanadi hukuncin daurin shekaru biyar ko tarar naira 10,000,000 ga wanda ya lika fostan yakin neman zabe a gida ko a shago ba tare da sanin mai wurin ba, da dai sauran sashi da suka tanadi hukunci ga masu karya dokar zabe.
Idan majalisa ta dawo daga hutu a ranar 20 ga watan Satumbar 2022, za a gudanar da karatu na uku game da wannan kuduri tare da tura kudurin ga majalisar dattawa kafin gabatar wa shugaban kasa domin ya rattaba hannu.