’Yan Majalisar Wakilai daga Kudu Maso Gabas sun roƙi Shugaba Bola Tinubu, ya yi wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan ta’addanci, afuwa.
Sun ce tsare Kanu na ci gaba da haifar da tashin hankali a yankin Kudu maso Gabas, kuma sakinsa zai taimaka wajen rage matsalar da ake fuskanta a yankin.
- Tinubu Ya Umarci A Janye Ƴansandan Da Ke Tsaron Manyan Mutane
- Ɗalibai Ƙarƙashin Tsarin Tallafi Na BEA Na Shan Wahala A Ƙasashen Waje
’Yan majalisar sun ce afuwar shugaban ƙasa za ta buɗe hanyar tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da shugabannin al’umma.
Sun kuma ce duk da suuna girmama hukuncin kotu, lamarin ya zama babbar matsala ta ƙasa da ke shafar tsaro, tattalin arziƙi, da rayuwar yau da kullum a yankin.
An yanke wa Kanu hukunci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, amma lauyoyinsa sun ce za su ɗaukaka kara.














