Connect with us

LABARAI

’Yan Nijeriya 12,797 Suka Mutu A Hadurra Cikin Wata 30

Published

on

Kididdiga daga hukumar kididdiga ta kasa, (NBS), sun nu na a shekarar 2016, jimillan ‘yan Nijeriya 5,053 ne suka mace a sanadiyyar hadurra a kan hanyoyinmu, a sa’ilin kuma da a shekarar 2017, jimillan ‘yan Nijeriya 5,121 suka mace a sanadiyyar hadurran.

Hakanan binciken ya nu na a farkon watanni shida na wannan shekarar ‘yan Nijeriya 2,623 duk sun mace a sanadiyyar hadurran da suka faru a kan hanyoyin namu.

A zango na biyu na 2018, sakamakon da hukumar ta fitar a jiya kan hadurran, ya nu na ‘yan Nijeriya 1,331, ne suka mace a wannan zangon, wanda ya haura mutane 1,292 da suka mace a zango na biyu na wancan shekarar.

Hukumar ta bayyana cewa, jimillan ‘yan kasar nan, 1,306 ne suka mace a hadurran hanyan a zangon karshe na shekarar 2017.

Har ila yau, rahoton ya nu na an samu hadurra, 2,608, a hanyoyin namu a zangon na biyu na 2018.

An sami rahotan keta haddin gudu ne babban dalilin da ke janyo hadurran a zangon na biyu na 2018, wanda ya kai kashi 50.65 na jimillan hadurran a hanyoyin namu.

Fashewar taya da tukin ganganci su ke biye da juna kusa da kusa, wanda suka yi sanadiyyar kashi 8.59 da kuma kashi 8.40 na jimillan hadurran.

Sannan rahoton ya nu na jimillan ‘yan Nijeriya 8,437 ne suka sami raunuka a hadurran hanyoyin, daga cikin su 7,946, duk manya ne, sauran kuma 491 din yara ne.

Sauran kididdigan ya nu na, ‘yan Nijeriya maza 6,415 ne suka sami raunukan, 2,022 kuma mata ne a zangon na biyu na shekarar ta 2018.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: