A ranar Laraba da ta gabata ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudade na Naira 200 da 500 da kuma 1,000, a fadarsa da ke Abuja.
Idan ba a manta ba dai, a ranar 26 ga watan Oktoban 2022 ne, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (DBN), Godwin Emefiele ya ayyana cewa babban bankin zai sauya fasalin Naira 200 da 500 da kuma 1,000 wanda za su fara aiki a ranar 15 ga watan Disambar 2022, yayin da za a daina amfani da tsofaffin takardun kudade tun daga ranar 31 ga watan Janairun 2023.
- Gudummawar Kamfanonin Fasahar Sadarwar Kasar Sin Ga Kara Dunkulewar Duniya
- Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da sabbin kudaden, Gwamnan CBN ya shaida wa manema labarai cewa an kaddamar da kudaden ne domin amfanar mutane.
CBN ya ce akwai alfanu sosai game da sauya fasalin takardun Naira wadanda ya kaddamar. Emefiele ya ce daga cikin alfanun da za a samu har da dakile yunkurin buga jabun kudi.
“Alfanun da za a samu na sauya fasalin Naira na da matukar muhimmanci ganin cewa yunkurin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi ta hanyar mayar da kudi zuwa bankuna.
“Sauyin zai tallafa wajen gyara fasalin kudin da kuma samun cikakkun bayanai game da zagayawar kudi a tsakanin jama’a.
“Mun yi imanin cewa hakan zai jawo karuwar jama’a cikin harkokin kudade da kuma rage amfani da sabar kudin.
“Sauya fasalin zai taimaka wajen yaki da rashawa saboda za a kara yawan manyan takardun Naira wadanda su kuma za a iya bin sawunsu daga bankuna cikin sauki,” in ji shi.
Cikin wadanda suka halarci kaddamar da sauya fasalin kudin sun hada da sakata-ren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari da shugabar ma’aikatan tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan.
Sauran sun hada da ministodo da gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Sakamakon wannan sauya fasalin takardun kudin, ‘yan Nijeriya da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Shehu Babayo ya bayyana cewa wannan matakin sauya fasalin kudin sanadiyyar arzikin wasu Kenan, sannan kuma sanadiyyar talaucewar wasu Kenan. Allah ya kara mana arziki masu albarka.
Shi kuma Uthman Eedrith ya bayyana cewa yanzu fisabillahi a kan wannan kalar da kuka goga wa kudin shi ne kuka tayar mana da hankali, wanda muka kasa za-ma ko da yaushe muna cikin razana, a she duk a nan za a kare. Wallahi na dauka wata kala mai kyau za a yi da ta sha banban da na da.
Yayin da Auwal Sani Yankaba ya ce A matsayina na dan kasa, ina ba da shawara a sake gyara 1000. Domin bai kamata a rubuta 1000 kawai babu alamar Naira ba, su 500 da 200 ai an saka musu. Yanzu wanda lambobi kawai ya iya karantawa ta ya ya zai gane Naira ce ko Sefa ce, ko kuma dala ce?
A cewar Abubakar Moh’d Idris, haba su kuwa, me ya sa ba za a dan sauya fasalin irin rubutun da ke jikin kudaden ba. Ya kamata da an dan kara wasu ‘yan abubuwa daya ko biyu a jikin kowanne takardan kudin. Kawai an canza fenti bayan komai yana nan kamar yadda yake. Kenan sai mutane su rina nasu su dunga bai wa mu-tane da daddare.
Auwal Abdurrahman Idris ya de Allah sarki kasata, abin da take so a yi mata ba shi ake yi ba. Ya mamallakin mutum da Aljan mai juya komai a karkashin mulkinsa muna dada tuba a gareka, ya Malikal mulki tutal mulka ka dube mu da rahamarka da jin kanka ga bayinka dikin matsi da kundin rayuwa ka yafe mana zunubanmu, ba dan halinmuba, sannan ka shirye mu zuwa biyayya agare ka, ka ceto mu, san-nan ka ceci kasarmu daga hannun azzaluman shugabanin kasarmu ta Nijeriya, domin mutundin Muhammadu Rasulullahi (S A W).
Wannan shi ne irin martani da wasu ‘yan Nijeriya suka bayyana a kan saurya fa-salin kudade da gwamnatin tarayya da kaddamar.