Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

’Yan Nijeriya Sun Fi So A Magance Rashin Tsaro Fiye Da Korona, Cewar Bafarawa

by Muhammad
January 21, 2021
in LABARAI
4 min read
Bafarawa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • A Juya Kuɗin Rigakafin Cutar Naira Biliyan 400 Zuwa Tsaro

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta sake shawara game da yadda ta mayar da hankali kacokan a kan yaki da cutar Korona fiye da tsaro a kasar nan. Inda ya ce mafi akasarin ‘Yan Nijeriya sun gwammace a magance musu matsalar tsaron da ke addabarsu fiye da cutar.

Ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru da ya gudanar jiya Laraba a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Bafarawa wanda ya nunar da cewa gwamnatin Buhari ta bar jaki tana dukar taiki a kan abin da ya fi dacewa ga kasa, ya kara da cewa: “Ina ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta mayar da hankali sosai a kan batun rashin tsaro da ya addabi kasa musamman a arewa a maimakon mayar da hankali da kashe makudan kudade a kan cutar Korona. A kwanan nan, kwamitin yaki da cutar ya ce ana bukatar Naira Biliyan 400 wajen sayo allurar riga-kafin cutar, baya ga Naira Biliyan uku da rabi (N3.5bn) da aka kashe a kan daukan matakan dakile ta. Shin ya kamata a bari hakan ta cigaba da faruwa, mun tsinci kanmu a wani yanayi da rayukan ‘Yan Nijeriya sun zama ba su da daraja. Zuwa yanzu akalla mutum 2,000 ne kacal aka ce Korona ta kashe a Nijeriya.” In ji shi.

“Kowanne a cikinmu ya kamata ya sa a zuci cewa a yayin da gwamnati ke yin abin da ya dace ta yi, mu ma ya dace a ga muna ba da gudunmawa wajen cimma muradin da aka sa a gaba na raba al’umma da wannan alkaba’in.”

“A yanzu haka da nake wannan maganar, akwai dubban daruruwan mutane da suka bar garuruwansu da suka gada iyaye da kakanni, sun tsere sun bar gidajensu, sun bar gonakinsu da dabbobinsu, wadanda suka ci sa’a ne kawai suka tsira da dan kadan. ‘Yan bindiga sun sace masu dabbobinsu. Don haka ya kamata mu sanar da gwamnati domin a dauki karin tsauraran matakai don magance bala’in da rashin tsaro ke haddasa wa al’ummarmu. Ya kamata mu dauki wannan batun da muhimmanci domin kar muna ji muna gani Nijeriya ta ruguje.”

Ya kuma bayyana cewa Nijeriya tana mayar da hankali a kan Korona ce domin neman suna kawai a tsakanin kasashen waje ba domin tana da matukar bukatar hakan ba, saboda haka ya yi kira ga gwamnati ta sake lale domin yi wa ‘yan kasa abin da ya fi dacewa.

Bafarawa, ya kuma nunar da cewa kwamitin da gwamnati ta kafa domin yaki da cutar ta Korona har yanzu yana cin tuwo da miyar bara, kasancewar babu wasu sababbin matakai da ya dauka baya ga umurnin a sanya takunkumi, a rika wanke hannu, a rika ba da tazara da rufe makarantu da sauransu.

“Har yanzu kwamitin yana aiki ne da wadannan matakan. Amma ya kamata a lura, a tsakanin wannan lokacin wanda bai wuce wata 9 ba zuwa yanzu, ko shekara ba a yi ba, an ce an kashe zunzurutun kudi Naira Biliyan uku da rabi. Wannan fa ba tare da an kebe kudi domin bincike ko wani yunkuri da ya shafi sayen magunguna ko bincike na kirkiro da magunguna ko sarrafa su ba ne.”

“Haka nan ya kamata a san cewa har yanzu akwai kudade da matakan gwamnati daban-daban da wasu kungiyoyi na duniya ke neman a sahale musu su kashe a kan cutar ta Korona. Da alama wannan aikin na Korona ya zama tagomashi ga wasu… kuma musamman a Nijeriya, saboda neman suna a idanun kasashen waje ko a ce yauwa kasar ta nuna damuwa a kan cutar,” in ji shi.

Alhaji Bafarawa ya kuma ce ba suna musun akwai cutar Koronar ba ce, amma a gaskiya an dauke ta da muhimmanci fiye da kima da kuma la’akari da abin da ya fi addabar kasar a halin yanzu.

“Na gabatar wa Shugaban Majalisa Rt. Hon. Gbajabiamila da takardun da suka kunshi bayanan kusan dukkan mutanen da ba kawai alkaba’in Boko Haram ya shafa ba har da na wadanda barnar ‘yan bindiga da sace mutane da garkuwa da su ta shafa a sashen arewacin kasar nan. A lokacin taron, na ja hankalin shugaban majalisar kan cewa yanayin kashe-kashe da barnar dukiyar da ake yi yana da matukar tashin hankali, sannan matukar ba a dauki kwakkwaran mataki na tsaro ba, ba za a samu zaman lafiya ba kuma idan babu zaman lafiya, babu wani cigaba da za a samu.”

Da LEADERSHIP A Yau ta tambaye shi, ba ya ganin gwamnati tana kokari kan daukar sabbin matakai tun da har ta ware sama da Naira Tiriliyan Daya a kasafin kudin 2021? Ya amsa da cewa, kasafin kudi hasashe ne ba wani abu ne na tabbas ba, sannan kudin da aka ce za a sayo riga-kafin Korona da su bashi aka ce za a nemo saboda muhimmancin abin, “to me ya sa bangaren tsaro ba zai samu irin hakan ba,” in ji shi.

Attahiru Bafarawa ya kuma bai wa gwamnati shawarar ta kara yawan jami’an tsaro ta hanyar la’akari da ‘yan sintiri da suke aikin sa-kai tare da horar da su don su taimaka, inda ya ce shi a shirye yake ya rika zuwa wuraren da za a horar da ‘yan sintirin don kara musu kwarin gwiwa.

SendShareTweetShare
Previous Post

NAF Ta Halaka ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Zamfara

Next Post

Fashewar Tankar Mai Ya Ci Rayuwar Mutum Uku Da Jittaka Shida A Ogun

RelatedPosts

Garkuwa

An Kama Sojan Da Ke Kai Wa ‘Yan Ta’adda Kayan Sojoji A Zamfara

by Sulaiman Ibrahim
1 hour ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim "An kama wani jami’in soja da budurwarsa...

Aikin Wutar Mambilla  A Takardu Kawai Yake, Inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

Aikin Wutar Mambilla A Takardu Kawai Yake, Inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun nuna rashin jin dadin...

Bindiga

Gwamna Ortom Ya Yabawa Umarnin Buhari Na Hana Mallakar  AK47 Ba Bisa Ka’ida Ba

by Muhammad
6 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom a ranar...

Next Post
Ogun

Fashewar Tankar Mai Ya Ci Rayuwar Mutum Uku Da Jittaka Shida A Ogun

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version