Matatar man Dangote da kungiyar dillalan Man Fetur a Nijeriya sun daura alhalin tashin farashin mai na baya-bayan nan da karuwar farashin danyen mai a kasuwar duniya, yayin da ‘yan Nijeriya suka koka da wannan karin.
‘Yan Nijeriya dai sun wayi garin ranar Juma’a da sabon karin kudin man fetur a fadin kasar nan, inda suka nuna hakan a matsayin koma-baya.
- A Shirye Kasar Sin Take Ta Kyautata Dangantakar Tattalin Arziki Da Amurka
- Yajin Aikin Likitoci Ya Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
Matatar mai ta Dangote ta kara farashin manta daga naira 899.50 kan kowace lita zuwa naira 950, inda ke nuni da an samu karin naira 50 wato kaso 5.
Bayan hakan, gidajen mai kuma sun kara farashin da suke sayar da litar mai kama daga naira 970 da naira 1,150 daga naira 935 zuwa naira 1,100 a kan kowace lita.
A wata sanarwar da kakakin matatar mai ta Dangote, Anthony Chijiena, ya fitar, ya yi bayanin cewa an samu karin farashin danyen mai a duniyance daga dala 70 zuwa dala 82 kan kowace ganga.
Ya ce, “Matatar Dangote ta dauki kusan kashi 50 cikin 100 na farashin da ake samu a kasuwannin mai na duniya. Wannan ya faru ne saboda jajircewar da muka yi na samar da man da inganci da arha, da kuma mallakar matatar man da ‘yan Nijeriya ke yi, wanda ya kasance jigon ayyukanmu. Idan matatar Dangote za ta kai duk wani karin farashin danyen mai zuwa kasuwa, farashin dillalan man zai kai kusan naira 1,150 zuwa naira 1,200 kowace lita a wasu wurare, idan aka kwatanta da farashin na naira 970 a halin yanzu.”
Su ma a bangarensu, PETROAN, ta cikin sanarwar da kakakinta, Joseph Obele, ya fitar, shi ma ya daura alhalin karin da tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.
Da yake nakalto abun da shugaban kungiyar PETROAN, Billy Gillis-Harry, ke cewa, tabbas tashin farashin dayen mai a kasuwar duniya zai shafi tace mai a Nijeriya.
“Tabbas tashin da saukar farashin mai na shafan gidajen manmu. Kuma yana shafan kasuwancinmu ma.
“Ko da yaushe farashin da muka sayar da kayanmu na samu asali ne daga yadda muka saya. Don haka, ka da a zargi mambobinmu da karin kudin mai da ake fuskanta a halin yanzu,” ya shaida.
Sai dai kuma ‘yan Nijeriya da dama sun nuna matukar damuwarsu kan wannan lamarin. Farfesa Theophilus Ndubuaku, ya ce, sabon karin kudin mai tunin ya shafi farashin kayan abinci da kudin sufuri.
Suleiman Abubakar, mazaunin Abuja, ya ce kwanakin da ke gaba za su zama masu wuya ga al’ummar kasa sakamakon wannan karin kudin Lltar mai da aka samu.