Jigon PDP, Sule Lamido, ya zargi gwamnatin tarayya da kuma jam’iyyar APC da yaki don aljihunsu yayin da ‘yan Nijeriya ke fama da bakar wahala.
Tsohon gwamnan Jigawa, wanda ya yi magana a babban taron PDP a Dutse, ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari da ta Bola Tinubu sun yi wa ‘yan Nijeriya zagon kasa da kuma jefa su cikin kunci.
- Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Nijeriya Sun Koka Kan Rashin Biyan Basussukan Albashi
- Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)
A cewar Lamido, duk da cewa gwamnatin tarayya da mambobin APC suna ikirarin suna yaki ne don ‘yan kasa, suna yaki ne kawai don kansu da kuma aljihunsu.
“Tun lokacin Buhari har zuwa yanzu lokacin Tinubu, ‘yan Nijeriya na cikin wahala. Talauci tana nan a ko’ina, matasa ba su da aikin yi, kuma tattalin arziki yana lalacewa. Su na cewa suna yaki don Nijeriya, amma a zahirin gaskiya, suna yaki ne kawai don kansu da aljihunsu.
“Na kasance cikin gwagwarmaya tun daga shekarun 1970. Na san ma’anar yakki don samun dimokuradiyya da kuma don talakawa. Gwamnatin Tinubu, kamar dai gwamnatin Buhari take ta gaza warware matsalolin ‘yan Nijeriya. Maimakon a samu sauki, sai aka samu karuwar cin hanci da rashawa da wahallalu da kuma amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba,” in ji Lamido.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp