Kungiyar Fulani Makiyaya Miyetta Allah, ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a Jihar Sakkwato sun halaka mambobinta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.
Shugaban kungiyar ta kasa, Baba Usman Ngelzerma ya ce wannan rikici ya barke ne tun a ranar juma’a sakamakon harin da tawagar ‘Yan sa-kan suka kai matsugunan makiyayan, abin da ya kai ga rasa rayuka da kuma kona rugagen Fulanin.
- Bangaren Hada-hadar Kasuwanci Ta Yanar Gizo Na Kasar Sin Ya Bunkasa A Cikin Watan Maris
- Firaministan Malaysia: Shawarar Wayewar Kan Kasa Da Kasa Za Ta Taimaka Wajen Tinkatar Matsaloli
Ngelzerma ya ce daga cikin matsugunan Fulanin da aka kai wa hari sun hada da Tsola da Asara da Karan biki da kuma Sakamaro duka a yankin Gwadabawa, kuma an jikkata mutane da dama.
Jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da barayin shanu, abin da ya sa wasu al’ummomi suka kafa kungiyoyin Sa-kai domin taimaka wa jami’an tsaro kare lafiya da dukiyoyin jama’a.
Lokaci zuwa lokaci ana samun arangama tsakanin Fulani makiyayan da ‘Yan sa-kai abin da ke kai ga rasa rayuka.
Shugaban kungiyar Fulanin na kasa, Baba Usman Ngelzerma ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen dakile wannan matsala da kuma hukunta duk wadanda aka samu suna da hannu a ciki.