Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wani matashi dan shekara 28 da ya tsere daga gidan yarin Kuje mai suna Yakubu AbdulMumuni.
An kama wanda ake zargin ne a Sango-Ota, cikin karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar.
- Ya Kamata Buhari Ya Gaggauta Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU – Femi Falana
- Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa Ya Tsere Daga Kasar
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Oyeyemi ya ce an kama AbdulMumuni wanda aka samu da laifin hada baki da kuma kisan kai a jihar Kogi wanda kuma aka kai shi gidan yarin Kuje a ranar Litinin da ta gabata.
Oyeyemi ya ce an kama wanda ya tsere, mai shekaru 28, Yakubu AbdulMumuni, biyo bayan bayanan da ‘yan sanda suka samu a hedikwatar Sango-Ota cewa, an ga mai laifin a wani wuri kusa da Sango Ota.
“Bayan samun labarin, DPO mai kula da Sango-Ota, SP Saleh Dahiru ya yi gaggawar tara mutanensa, suka koma yankin da aka kama wanda ake tuhuma.
“Ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya tsere daga gidan yari na Kuje a ranar 5 ga watan Yuli, 2022, lokacin da Boko Haram suka kai hari.
“Ya kara da cewa babbar kotun jihar Kogi ce ta same shi da laifin hada baki da kuma kisan kai, aka tura shi gidan yari na Kuje.”
Sai dai kakakin, ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya umarci sashen binciken manyan laifuka na jihar da su maida mai laifin zuwa gidan yarin.