Daga Rabiu Ali Indabawa
Karar fashewar wani ta girgiza wata coci, Christian Universal Church International mallakar mahaifin Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, a Fatakwal, babban birnin jihar. Kafofin yada labaranmu sun samu labarin cewa da yawa daga cikin masu ibada sun tsallake rijiya da baya yayin jin karar fashewar. Rahotanni sun wannan al’amari ya gudana a daren kuma ya tayar da hankulan jama’a inda ke zargin bama-baman ne masu karfi.
A cewar rahotanni, wani muhimmin bangare na cocin ya lalace sakamakon fashewar, wanda ya haifar da tsoro a yankin. Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin aikata wannan mummunan aikin, amma an ce uku daga cikin masu laifin sun shiga hannun kungiyar ‘yan banga tare da mika su ga ‘yan sanda. A halin yanzu, ‘yan sanda sun tabbatar da cewa mutane ukun da a ke zargi da hannu a harin na Cocin suna hannunsu.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Nnamdi Omoni, ya ce wadanda ake zargin da aka kama suna taimaka wa ‘yan sanda a binciken da suke yi. Ya ce: “Zan iya tabbatar da harin da aka kai wa Cocin da kuma wasu mutane uku da ake zargi da hannu a harin. Suna taimaka mana a bincikenmu. Tawagar dake kula da Sashen aikin Bomb sun share Cocin ”.