Rundunar ‘yan sandan reshen Jihar Kano ta bayyana cewa, ta fasa wata kungiyar gungun masu aikata miyagun laifuka karkashin jagorancin tsohuwar mai aikata laifi, Hauwa Mustapha ‘yar shekaru 47.
Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Haruna, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce, wadanda ake zargin sun kware ne a harkar fashin motoci da fasa shaguna.
Abdullahi ya ce, “A ranar 19 ga Janairu, 2021, da misalin karfe 3 na dare, tawagar ‘Operation Puff Adder’ karkashin jagorancin CSP Alabi Lateef, yayin da suke gudanar da sintiri akan hanyar Zariya ta Kano, suka kama Hauwa Mustapha, ‘yar shekara 47, a ‘Naibawa Kuarters’, da ke Jihar Kano da wani mai suna, Auwalu Ibrahim, dan shekaru 28, a ‘Brigade Kuarters’ duk a jihar Kano, suna Mota da suka sata mai kirar Honda Accord da launin toka, suna tuki cikin dardar na rashin gaskiya.
“Bayan bincike, sai aka gano kayan aikin balle shaguna da motoci sinke a cikin bayan motar. Wadanda ake zargin sun amsa cewa sun hada baki da wasu mutum biyu, a yanzu haka, sun fasa wata motar da ke tsaye a kan hanyar Mariri Kuarters da ke jihar Kano, kuma sun saci katun 8 na gorunan ruwan ‘Swan’. Dukka masu aikata laifin sun amsa laifukansu kuma sun bayyana cewa dukkaninsu yaran tsohowar mai aikata laifin nan ne mai suna, Hauwa Mustapha. Ana cigaba da gudanar da bincike,” inji Abdullahi Haruna.