Ammar Muhammad" />

Yan Sandan Kasar Holland Sun Fara Binciken Wanda Ya Kai Hari A Jirgin Kasa

Hukumomin Kasar Nertherlands Sun Ce Su Na Farautar Wani Mutum Da Aka Haifa A Turkiya Kan Harin Da Aka Kai Utrecht A Jiya Litinin Wanda Ya Yi Sanadiyar Hallaka Mutum Guda.

‘Yan Sandan sun sanar da jama’ar birnin cewar, sun sanya ido kan mutumin Gokman Tanis mai shekaru 37 dangane da harin da aka kai jiya da safe.

Rahotanni sun ce dan bindigar ya bude wuta kan jama’a inda ya kashe mutum 3, ya kuma jikkata kalla guda 5.

Firaminista Mark Rutte ya bayyana harin wanda ke zuwa kwanaki kafin zaben kasar a matsayin abin tayar da hankali.

Exit mobile version