Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rundunar ‘yan sandan dake aiki a kan teku sun kashe wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashin teku ne wadanda suka kware a harkar ta’addancin masunta a hanyoyin ruwa na Ibeno, Akwa Ibom a musayar wuta. Kakakin rundunar, SP Macdon Odiko ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar kakakin rundunar, ‘yan fashin da ke dauke da muggan makamai sun yi artabu da tawagar’ Special Force Skuad ‘ a yayin artabun da suka saba yayin sintirin jami’an tsaro a hanyoyin ruwa. “Labarin gaskiya ne amma nan ba da jimawa ba zan fitar da sanarwa don tabbatar da hakan, ”in ji Odiko.
Da yake magana kan ci gaban lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Ibeno, Williams Mkpa shi ma ya tabbatar da kisan ‘yan fashin, ya kuma yaba wa mambobin runduna ta musamman kan nuna kwarewa.
Ya kara da cewa fashin kan tekun ya kasance babbar matsala da ke hana kasuwancin kamun kifi da sauran ayyukan tattalin arziki a Ibeno. Mkpah ya nuna damuwa kwarai kan yanayin rayuwa mara kyau a Ibeno kuma, yana mai cewa al’amari ne da ke ciwa yankin tuwo a kwarya.
Ya nanata cewa ba zai iya zama Shugaban Karamar Hukumar ba sannan ya zauna yana kallon mutanen sa suna wahala ba tare da Daukar kwararan matakai don kiyaye hakkokinsu ba.
“Filin nomarmu shi ne ruwa. Da zarar kun kwace mana gonarmu, hakan na nufin ba za mu sake yin aiki ba, yana nufin kun kwace ayyukan mutanen Ibeno da kashe mu a faikaice,” inji Mkpah.
“Mun sha wahala sosai a hannun ‘yan fashin teku. Za su afkawa mutanenmu, su kwace kwale-kwalensu da injunansu kuma za su nemi fansar kudin da ta kai miliyoyin naira kafin ka dawo da jirginka da injinka. Wani lokaci, za su sace masu mallakar tare da kwale-kwalensu da injinansu.”
Da yake amsa tambayoyin kan yadda ya sami damar farawa da kawo ‘Runduna ta Musamman’ zuwa Ibeno. Mkpah ya ce “Wannan rundunar ana kiranta ‘Runduna ta Musamman. Sun kware ne a harkar tsaron teku. Watanni da suka gabata, a cikin sha’awar na sanya Ibeno ta kasance yanki mai tsaro da aminci ga harkokin kasuwanci, na kaddamar da wannan rudunar Tsaro ta Musamman don Kulawa da kiyaye layinmu wanda kuma wannan shi ne sakamakon da muka fara gani, ”
“Na samar da rukuni 4 na injunan ‘Horsepower’ 200, rukuni 2 na injunan Horsepower’ 75 da kwale-kwalen gudun masu sintiri na jami’an tsaro guda biyu tare da karin injinan Horsepower’ 200 da kuma ba da kulawa ga jirgin ruwa wanda ke a matsayin tanadi.”
Mkpah, ya bayyana cewa ‘yan fashin teku inda masunta suka hango Gabashin obolo Escrabos a kokarin afka musu, wanda nan take suka sanar da rundunar ta musamman kuma, ta hanyar musayar bindiga, suka ci karfin’ yan fashin suka bar mutane hudu, yayin da daya ya samu nasarar don tserewa da raunin da ya samu.
An kwato Horsepower’ 200, na Jirgin ruwa mai gudu guda daya, jigidar AK 47 gami da ‘setima riffle’ da sauran manyan makamai da carbin harsashi daga masu satar a teku.
A halin yanzu, Mkpah ya bukaci ‘yan asalin yankin da kuma mazauna Karamar Hukumar da su kwantar da hankulansu tare da gudanar da ayyukansu na yau da kullun ba tare da fargaba ba, yana mai ba su tabbacin samun tsaro, da zaman lafiya da kwanciyar hankali.