• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 3, Da Sace Wata Mata A Katsina

"Yanzu sun gwammace su kai hari da rana saboda suna da masaniyar cewa mutane da yawa sun je gona wasu kuma kasuwa don neman abincin yau da kullun."

by Muhammad
3 years ago
'Yan

Kimanin mutane uku ne aka kashe a kauyen Bakiyawa da ke karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka mamaye yankin.

Wata majiya ta bayyana cewa an harbe wani mutumin kauyen a kafa yayin da wata matar aure mai suna Hawawu Yusuf ‘yar Ungwar Makera kuma maharan suka yi garkuwa da ita.

  • Al’umar Mai’adua Na Bukatar Gyaran Masallacin Juma’arsu Da Ya Shafe Shekaru Ba Gyara

A cewar majiyar wanda mazaunin unguwar ne, maharan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, inda suke kan babura, inda suka yi nasarar kai harin na kusan mintuna 30 a yankin.

Ya kuma bayyana sunayen wadanda aka kashe a harin da suka hada da Aminu Abdulwahab da Musa Abubakar sai Sadiq Lawal.

Majiyar ta bayyana cewa: “A ‘yan kwanakin nan muna ganin yadda ‘yan bindiga suka kai hari a yankinmu. A dai dai mako guda da ya gabata da misalin karfe 2:30 na rana, ‘yan bindiga sun kai hari a unguwarmu tare da yin garkuwa da mutane shida. Wadanda aka kashe din dai har yanzu suna cikin dajin kasancewar babu wanda aka sako daga cikinsu.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

“A ranar Lahadi kuma, an yi garkuwa da daya daga cikin matasan unguwar kuma har yanzu ba a sake shi ba. A jiya Litinin da karfe 4 zuwa 4:30 na yamma, ‘yan bindigar sun sake kai farmaki cikin jama’ar inda suka kashe mutane uku.” Cewar majiyar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda
Labarai

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi
Manyan Labarai

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
Next Post
Majalisar Dattawa Zata Tantance Sunayen Ministocin Buhari Ranar Laraba Mai Zuwa

IMF

Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF

October 18, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
katsina

Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu

October 17, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari

October 17, 2025
Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.