Wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a kauyen Garjang da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno.
Majiyoyi, a cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi.
- Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki A Taraba
- Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19
Wanda aka kashe mai suna Habu Dala mai shekaru 53, ‘yan ta’addan ne suka dauke shi daga gidansa, inda suka bi da shi ta hanyar Mulharam zuwa kauyukan Forfot da ke karamar hukumar Damboa.
An tattaro jama’ar kauye ne domin neman Dala amma daga baya suka tarar da gawarsa dauke da raunukan harbin bindiga, inda Dakarun Operation Hadin Kai, ‘na Civilian Joint Task Force (CJTF)’, da kuma ‘yan kungiyar mafarauta suka ziyarci wurin.
An kai gawar mafaraucin da ya rasu zuwa babban asibitin Damboa, inda aka tabbatar da mutuwarsa, daga bisani kuma aka mika shi ga iyalansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp