Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Taratsin Neja Delta Sun Yi Zanga-zangar Rashin Biyansu Albashi

Published

on

Wadansu daga cikin ‘yan taratsin Neja Delta sun toshe yanyar gabas maso kudu inda suka jawo cinkoson ababan hawa na awoyi ranar Litinin. Majiyarmu ta bayyana mana cewa musabbin zanga-zangar dai shi ne rashin biyansu albashinsu na shirin afuwa da tsohun shugan kasa ya yi masu. Tsohun jagoran ungiyar wanda yake zaune a Mbiama iyakar Jihar Ribas da kuma Jihar Bayelsa, ya yi kira ga gwamnati da ta saka baki a kan lamari. Tsofaffin ‘yan ungiyar sun bayyana cewa za su yi mummunar zanga-zanga a cikin garin Abuja in har gwamnatin tarayya ba ta auki matakin dakatar da shugaban gudanarwa Charles Dokubo. Suna dauke da kulaye wadanda aka rubuta cewa, “ku biya mu kudinmu” “jami’an Amnesty ku biya mu kudinmu” da dai suran su. Daga baya dai an dauki matakin tura jami’an soji, inda aka bawa Tari Parri umurni da ya shawo kan masu zanga-zanga kafin awa uku.

Shugaban masu zanga-zangan wanda aka fi sani da suna General Cairo, ya bayyana cewa an kasa cika masu alkawari duk da sun ijeye makamansu a shekara 2011. Cairo kara da cewa a kan alkawarin da aka yi musu, ya sha bakar wahala a tsawon shekaru hudu da ya yi a tsare.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: