Hukumar kandagarki da takaita yaduwar cututtuka ta kasar Sin ta ce yanayin yaduwar cutar kanjamau ya sauka kasa sosai a kasar, bisa yadda aka magance yaduwar cutar ta hanyar karin jini da takaita yaduwarta daga uwa zuwa da, da kuma ta hanyar allura.
A jiya Litinin ne aka yi bikin ranar kanjamau ta duniya, inda albarkacin ranar, Xia Gang, daraktan hukumar ya ce bisa jajircewarta cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu nasarori a bangaren takaita yaduwar cutar da ma jinya.
Ya kara da cewa, bisa ingantuwar tsarin kandagarki da na jinya, da ingantattun fasahohi da karin hidimomin da ake iya samu, adadin mace-macen da cutar ke haifarwa ya ragu da kaso 86 idan aka kwatanta da shekarar 2003. (Mai fassara: FMM)














