Ma’aikatar cinikayya ta Sin ta ce yankunan raya tattalin arziki na matakin koli na Sin sun samu bunkasar GDP bisa daidaito a shekarar 2022, inda suka samu karuwar kaso 5.6 bisa dari a shekara guda.
Yayin taron manema labarai da ya gudana, kakakin ma’aikatar He Yadong, ya ce a shekarar 2022 darajar GDPn yankunan 230 dake sassan kasar daban daban, ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 14, kwatankwacin kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.97, adadin da ya kai kaso 12 bisa dari na jimillar GDPn kasar baki daya.
- Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Da Abubuwan Da Kasar Sin Za Ta Yi A Fannin Harkar Diplomasiyya A Shekarar 2024
- Kotu Ta Bai Wa Trump Damar Shiga Zaben Fidda Gwani A Amurka
He Yadong ya kara da cewa, a tsakanin wa’adin, adadin jarin waje da aka yi amfani da shi a yankunan ya karu da kaso 11.5 bisa dari, inda ya kai dala biliyan 43.2, wanda ya kai kaso 23 bisa dari na jimillar wanda kasar ta samu.
Bugu da kari, jami’in ya ce a shekarar ta 2022, hada-hadar cinikayya a yankunan raya tattalin arziki na matakin koli na Sin ta kai darajar yuan tiriliyan 10.3, adadin da ya karu da kaso 15 bisa dari, ya kuma kai kaso 25 bisa dari kan jimillar na kasar baki daya. (Saminu Alhassan)