Rundunar ’yansandan Jihar Adamawa ta tabbatar da kama mutane tara da ake zargi da hannu a kisan wani jigo na jam’iyyar PDP, Mista Thomas Godwin, wanda aka fi sani da Zamfara.
Kakakin ’yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan wani faifan bidiyo da ya yaɗu a yanar gizo, inda wasu daga cikin waɗanda ake zargin suka ce an azabtar da su, an hana su abinci kuma an tilasta musu amsa laifin da ba su aikata ba.
- ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME.
- Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
Nguroje ya ce binciken da suka fara game da kisan ya kai su ga kama mutum tara.
Waɗanda aka kama sun haɗa da: Sunday Terrang, Umar Ibrahim, Sadiq Ishaku, Solomon Gideon, Ahmed Aminu, Danlami Ali, Godwin Chakukuyada, Akacha Daniel Samari da Ibrahim Bakari.
Bayan kammala binciken farko, an tura su zuwa sashen rundunar IRRT da ke Abuja don ci gaba da bincike.
Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar.
Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata suna da amincin rundunar.
Nguroje ya yi gargaɗi game da yaɗa labaran ƙarya da ka iya janyo cikas ga binciken da ake yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp