Rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna ta ce ta kama wasu Fitattun masu garkuwa da mutane hudu, tare da kwato bindigogi da suka hada da bindiga kirar AK47.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna, ASP Munsir Hassan ya fitar, ta bayyana cewa a ranar 29 ga watan Mayun 2024, bisa wani rahoto da aka kai wa rundunar da tawagar kungiyar mafarauta a Saminaka da ke karamar hukumar Lere ta Jihar, ta yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane da satar shanu.
Wadanda ake zargin sun hada da Isah Baffa Rabo, mai shekaru 30; Ja’afaru Sale mai shekaru 30; da Umar Musa mai shekaru 24.
Rundunar kuma ta sake yin nasarar cafke wani Hussaini mai shekaru 70 a Tudun Jukun a Zaria
Talla