Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ta ceto mutum 21 da aka sace tare da ƙwato Naira miliyan 4.8 da ake zargin kuɗin fansa ne a jerin samame da suka gudanar a faɗin kasar.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce jami’an ‘yan sanda a Jihar Taraba, sun ceto mutum 20 daga hannun masu garkuwa da mutane a ranar 29 ga watan Maris, a kan titin Takum/Mararaba, bayan musayar wuta da ‘yan ta’addan.
- Tawagar Aikin Ceto Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin Ta Isa Myanmar
- Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
Mutane biyu sun jikkata, kuma ana kula da su a asibiti.
A Kano, ‘yan sanda sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a sace Dokta Muhammad Bello Yushau a ranar 8 ga watan Maris.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Tukur Lawal (Maikudi), Ado Usman, Sanusi Surajo, Habiba Shuaibu, da Ummulkhairi Ibrahim.
Haka kuma, an Ƙwato bindiga ƙirar gida da Naira miliyan 4.84 da ake zargin kuɗin fansa ne.
An ceto Dokta Yushau ba tare da wata matsala ba.
A wata arangama daban, jami’an ‘yansanda sun kama wani Kafinta Musa a Jihar Taraba bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
An ƙwato bindiga ƙirar AK-49 a hannunsa, kuma ana ci gaba da bincike don kama sauran miyagun da ke tare da shi.
Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da wannan aikin tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp