Rundunar ‘Yansanda a Jihar Kaduna ta hana gudanar da taron da magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka shirya don bikin zagayowar ranar haihuwarsa a jihar.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ‘yansandan sun bayyana cewa za su kama duk wani mutum ko ƙungiya da ta ci gaba da shirya taron duk da umarnin haramta taron.
- 2027: Atiku, Obi Da Amaechi Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Takarar Shugaban Kasa A ADC
- Peter Obi Ya Kai Wa Iyalan Buhari Ziyarar Ta’aziyya
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce bincike da rahotannin sirri sun nuna cewa “wasu miyagu na shirin fakewa da taron domin tayar da fitina da haddasa tashin hankali da kuma tayar da rikici a jihar.”
Rundunar ta kuma bayyana cewa lokutan taron sun yi karo da zaɓen fidda gwani na wasu jam’iyyun siyasa da aka riga aka sanarwa ‘yansanda su kamar yadda dokokin Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) suka tanada.
“INEC ta tsara zaɓen fidda gwani na zaɓen cike gurbi a ranar da aka shirya gudanar da taron Peter Obi, kuma jam’iyyun siyasa sun riga sun sanar da ‘yan sanda kamar yadda doka ta tanada,” in ji sanarwar.
‘Yan sandan sun ƙara da cewa “taron zai iya hana gudanar da zaɓen fidda gwani a wuraren da aka ware, kuma hakan na iya janyo rikici da tashin hankali.”
Duk da cewa ‘yan ƙasa na da ‘yancin taruwa da nuna ƙauna ga shugabannin siyasa, ‘yan sanda sun ce har yanzu tarukan siyasa a jihar an dakatar da su har sai INEC ta sanar da fara kamfen ɗin siyasa.
Rundunar ta yi kira ga masu shirya taron Obi da su soke taron domin gujewa barazana da zaman lafiya da kuma kauce wa masu garkuwa da mutane.
DSP Hassan ya ce rundunar za ta ɗauki matakin doka kan duk wanda ya saɓa da wannan umarni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp