‘Yansandan sun samu nasarar kama mutum goma sha bakwai da ake zarginsu da laifin yin garkuwa da mutane Jihar Filato da Bauchi.
Rundunar ‘yansandan ta nuna wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yansanda da ke Jos.
- Obasanjo Ya Roki Marayun Borno Su Yafe Wa ‘Yan Ta’addar Da Suka Kashe Iyayensu
- Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Filato, Mista Bartholomew Onyeka, ne ya bayyana haka, sannan ya ce, kafin shigarsu hannu, sai da suka yi ta kullu-kuciya da su tun daga Yuni zuwa wannan wata na Agusta wadanda karshensu ya zo.
Daga cikin wadanda aka kaman akwai mutun biyu, wadanda bayan yin garkuwa da mutanen da kuma ‘yan fashi da makami ne.
Onyeka ya ce: “Rundunar ‘yansanda na musamman da ke yaki da masu manyan laifuka ta gudanar da wani bincike, wanda sakamakonsa aka kama Haruna Hamisu.
Lokacin da ake bincikensa ya tabbatar da cewa, yana daga cikin wadanda rundunar ke nema ruwa a jallo kasancewarsa daya daga cikin jiga-jigan masu garkuwa nda kuma fashi da makami a kan hanyar Jengre zuwa Saminaka.
Sakamakon bayanan sirrin da aka samu daga wajensa ya sa jami’an ‘yansanda masu yin bincike na musamman, suka bi sawu zuwa maboyarsu da ke dajin Kudaru suka kama Umaru Hassan da Rufai Hasimu da Adamu Ali, 21 wadanda dukkansu ‘yan kauyen Igabi ne ta jihar Filato.
Onyeka ya ce an kama su da bindigogi guda hudu da harsasai.
Haka kuma ya ce, a wani samamen da suka sake kai wa, sun kama Mohammed Ibrahim.
A karshe, ya rundunar ‘yansandan na ci gaba da bincike, wanda bayan kamma binciken nata za ta gurfanar da wadanda ake zargin gaban alkali.