Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa, ta kama wani matashi da ake zargi da kashe mahaifinsa a garin Sara, da ke karamar hukumar Gwaram.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, inda matashin ya sassari mahaifinsa har ya mutu.
- Aikin Hajjin 2025 Ya Fara A Hukumance Yayin Da Tawagar NAHCON Ta Musamman Ta Tashi Zuwa Makkah
- Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta
Bayan faruwar lamarin, an yi jana’izar mamacin yayin da ɗan nasa ke hannun ‘yansanda.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya ce lokacin da jami’ansu suka isa gidan, sun tarar da mamacin kwance cikin jini.
“Ya sassari mahaifinsa a kafaɗa, ya yanka maƙogwaronsa har ya kai kirjinsa. Nan da nan aka kai shi asibiti a Birnin Kudu, inda aka tabbatar da mutuwarsa,” in ji SP Shi’isu.
Ya ce an kama matashin tare da addar da ake zargin ya yi amfani da ita, kuma yanzu ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ya aikata hakan.
“Matashin yana hannunmu, kuma muna ci gaba da gudanar da bincike,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp