Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce, ta samu nasarar kama mutum 45 da ake zarginsu da aikata laifin garkuwa da mutane da shiga kungiyar asiri da kisan kai da wasu manyan laifuka.
Mataimakin kwamishinan ‘yansanda na jihar Ajina Musbahu,da ke kula da sashin yaki da masu laifukan, ya bayyana haka lokacin da suka kai wani samame a Yola ta jihar Adamawa.
Ya ce, dukkan wadanda ake zargin za a yahke musu hukunci bayan kammala bincike.
“A cikin wata daya mun samu nasarar kama mutum 45 masu laifi, wadanda suka hada da masu garkuwa da ‘yan kungiyar asiri da masu kisan kai da masu fyade da barayin masu shiga gidaje da kuma wasu sauran barayia fadin jihar,” In ji shi.
Musbahu ya kara da cewa, jami’an kayan da suka kama daga wadanda ake zargin sun hada da: kudi naira 900, 000 da mota daya da bindiga kirar gargajiya guda biyu da karamar bindiga guda daya da harsasai guda takwas da sauran wasu abubuwa da suke amfani da su wajen aikata laifuka.
Sannan kuma ya yaba da kokarin da gwamnatin tarayya da kuma sauran al’umma da ke fadin jihar wajen bayar da gudummowa kan harkokin tsaro.
Haka kuma Musbahu ya tabbatar wa da al’umma cewa, ‘yansanda za su ci gaba da yaki da bata-gari a duk inda suke a fadin jihar.
Sabo da haka ya bukaci dukkan jami’an tasaron su kara tasaurara tsaro, domin al’umma su samu damar walwala a duk inda suke.