Rundunar ‘Yansandan Jihar Kogi, ta bukaci mazauna yankin da su yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo, kan batun wani harin ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda na shirin kai wa, musamman a yankin Kogi ta Gabas.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Naziru Bello Kankarofi ne ya bayyana haka, a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, CSP William Aya ya fitar a daren ranar Litinin.
- Tsohon Gwamnan Kaduna, El-Rufai, Ya Fice Daga SDP, Ya Koma ADC
- Dambarwar Amurka Da Sace ‘Yan Makarantar Kebbi Da Neja: Shugaba Tinubu Ya Yi Rawar Gani
Ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe, ballantana asali.
Sai dai, rundunar ‘yansandan ta tabbatar wa da jama’a cewa, an samar da dukkanin matakan da suka dace, domin dakile dukkannin wata matsala ta tsaro a fadin jihar.
Har ila yau, sanarwar ta ce; “Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu tare da tabbatar da bayanai ta hanyar majiyoyin hukuma, kafin su kai ga yarda da su.
Ya kara da cewa, ya kamata mazauna yankin; su hanzarta kai rahoto ga hukumomin tsaro tare da lura da cewa; “tsaro alhakin kowa da kowa ne.”
CP Kankarofi ya bayar da umarnin tura tawagogin sanin makamar aiki, ciki har da rundunar ‘yansanda ta wayar tafi-da-gidanka, sashen yaki da ta’addanci da sassan leken asiri zuwa wurare masu mahimmanci a fadin jihar.
A cewar sanarwar, an kuma aike da karin wasu karin muhimman kayayyakin tsaro zuwa yankunan da suke da rauni, domin mayar da martani ga duk wani abu da ka iya bijirowa.
Kwanaki dai, kafafen sada zumunta na yanar gizo, sun yi ta yawo da ikirari na harin ‘yan bindiga da ke shirin kai wa a Kogi ta Gabas, bisa zargin “rahoton sirri na ‘yansanda” da ke yawo a tsakanin jami’an tsaro.
Rahoton da aka yada ya bayyana cewa, ‘yan bindiga sun kutsa cikin jihar daga Nasarawa ta Karamar Hukumar Bassa da kuma Jihar Benuwe ta Agatu da Bagana a Karamar Hukumar Omala.
Kazalika, an kuma yi zargin cewa; daliban jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Anyigba (PAAU) da makarantar sakandire ta Ochaja da ke Karamar Hukumar Dekina da kuma wasu sassan garin Anyigba ne aka kai harin.
Rundunar ‘yansandan ta sake nanata cewa, babu kamshin gaskiya a wannan labarin, inda kuma ta bukaci daukacin al’umma da su yi watsi da ire-iren wadannan jita-jita.














