ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dambarwar Amurka Da Sace ‘Yan Makarantar Kebbi Da Neja: Shugaba Tinubu Ya Yi Rawar Gani

by Bello Hamza and Sulaiman
8 months ago
Amurka

A ‘yan kwanakin nan ne kasar nan ta fuskanci dambarwa daban daban, cikinsu akwai batun zargin kisan kiyashi da shugaban kasa Amurka Donal Trump ya yi wa Nijeriya na kisan kiyashi ga al’ummar Kirista da kuma yadda ‘yan ta’adda suka sace ‘yan mata a makarantar da ke garin Maga ta Jihar Kebbi da kuma wata makaranta a Jihar Neja. Lamarin ya bayyana irin yadda shugaban kasa da wasu Minjstocinsa suka jajirce wajen ganin an samu nasara a dukkan bangarorin. A wannan hirar da Editanmu Bello Hamza ya yi wani mai fashin baki a harkokin yau da kullum, Kwamrade Bishir Dauda ya bayyana irinin kokarin da gwamantin Nijeriya ta yi. Ga dai yadda hirar ta kasance.

 

Ka ɗan gabatar mana da kanka

ADVERTISEMENT

Sunana Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, dan rajin kishin Afirika, Dimokaradiyya, hakkin dan Adam da shugabanci nagari. Nine shugaban Kungiyar wayar da kan al’umma a kan yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya mai suna ‘Citizens Participation Against Corruption Initiatibe’.

 

LABARAI MASU NASABA

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

Menene ra’ayinka a kan yadda Nijeriya ta fuskanci dambarwar zargin Kisan Kare Dangi daga Amurka?

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya nuna kwarewa da gogewa , kuma ya nuna tsinkaye da hangen nesa . Duk da kalamai na batanci ga Nijeriya da kokarin tunzura al’umma da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ke ci gaba da yi a kan kasarmu; bai sanya Shugaba Tinubu ya rude ba ko ya mika kai bori ya hau. Maimakon ya biye mai, sai mu ka ga abin da kowa bai zata ba: Cikin hikima da nuna dattako, Nijeriya ta karyata Shugaba Trump. Maimakon zage-zage da maida raddi mai zafi, sai Nijeriya ta yi amfani da kwararan hujjoji, ta nuna ikirarin Shugaba Trump soki-burutsu ne, karya ce tsagwaro Wannan irin salon Difilomasiyya da Nijeriya ke nunawa ga shugaba mafi hatsari a duniya  in ka cire Benjamin Netanyahu da Bladmir Putin, ya jawo ma Nijeriya kima a idon duniya . Mun ga yadda kasar Sin ta nuna tana tare da Nijeriya. Mun ga martanin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirika ta  ECOWAS , kungiyar tarayyar Afirika (A.U.) da sauran kasashen duniya.

Kazalika, mun ga yadda shugaba Tinubu ya tura tawaga mai karfi  karkashin mai bada shawara a kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu in da su ka je can kasar Amurka suka kuma gana da manyan jami’an gwamnatin kasar ciki har da dan majalisa Riley Moore da sakataren yaki da sauran su. Kuma Alhamdulillah, kwalliya ta biya kudin sabulu. Sun fahimci karya da furofaganda da ‘yanci da addini da kungiyoyiyn ina da kisa na IPOB suka kitsa. Kuma duniya ma fahimci hakan.

 

Barazanar Donald Trump ta tona asirin makiya Nijeriya ciki da waje. Saboda duk wanda zai kai kasarshi ta haihuwa kara zuwa wata kasa, kuma har ma ya fito yana kiran waccar kasar ta kawo hari, to wannan babban makiyi ne. Marasa kishin kasa ne kawai za sui alfahari da wata kasa tai katsilandan a cikin kasarsu.

Wani abin takaici shi ne, yadda wasu makiya Nijeriya ke nuna Katsinlandan din wata kasa a kasarmu shi ne zai magance matsalolinmu. Wannan tunani ne na makirai, masu ra’ayin mamaya. Katsinalandan din Amurka ko wata kasa a Nijeriya baida bambanci da  goyan  bayan mulkin mallaka. Kasan tarihi ya nuna ko lokacin da turawan mulkin mallaka suka zo mamaya, sai da aka samu munafukai wadanda suka mara masu baya. To irin haka ne. Munafikai masu ci da addini da ‘yan kungiyar aware ta Biyafara sune yanzu ke kira da a kawo hari a Nijeriya domin su dillalai ne na kasashe ‘yan mamaya da danniya, kuma biyan su ake.

Wani gudummawa manyan jamian gwamnatin tarayya suka bayar a kan lamarin (Ministan harkokin kasashen waje da mai ba shugaban kasa shawara a bangaren tsaro).

Dole mu jinjina wa mai ba shugaban kasa shawara a kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ministan harkokin kasashen ketare Yusuf Maitama Tugga, ministan yada labarai da sauya dabi’un ‘yan kasa, Alhaji Mohammed Idris da hadiman shugaba Tinubu irin su Bayo Onanuga, Abdul’aziz Abdul’aziz da dimbin mutane ma wadanda ba su rike da mukaman gwamnati, wadanda suka nuna su ‘yan halas ne Misali, Femi Fani Kayode, Omokri, Senata Shehu Sani da sauran su. Mun ga tasirin ganawar Nuhu Ribadu da Jakadan kasar Sin Yu Dunhai. Sannan mun ga yadda Ministan yada labarai Mohammed Idris da Abdul’aziz Abdul’aziz suke kokari babu dare ba rana wajen hira da manyan kafofin yada labarai na duniya domin fitar da gaskiya. Rawar da wadannan bayin Allah suka taka, ta taimaka kwarai wajen karya lagon dillalan kasashe ‘yan mamaya.

 

Ya kuma ka ga yadda gwamnatin tarayya ta tafiyar da batun sace daliban makarantar Kebbi da Neja da Kwara?

Shugaban kasa ya nuna damuwarsa. Ka ga farko da aka sace dalibai a Kebbi,ya tura mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima . Sannan kuma ya sake tura ministan tsaro.Yanzu haka har zuwa lokacin da muke wannan tattaunawa da kai, ministan tsaro, Bello Muhammad yana Jihar Kebbi ya tare domin tabbatar da an ceto yaran nan. Sannan a karon farko, a tarihin Nijeriya, shugaban kasa ya soke tafiyar da ya yi niyyar zuwa kasar Afirika ta Kudu domin halartar taron kasashen kungiyar G20. Mun ga yadda ya damu sosai. Dama matakan daukar karin jami’an ‘yansada dubu 30 da ba da ummarnin dawo da ‘yansandan da ke gadin masu mulki da attajirai .

To amma kash, duk irin wadannan kwararan matakai, ba su gamsar da wasu ‘yan siyasa wadanda suke ganin wannan matsalar dama ce ta su ci zabe. Wadannan manyan ‘yan siyasa masu farin ciki an sace dalibai da murnar Trump zai kawo mamu hari, In Sha Allah, za su ji kunya. Domin da iznin Allah za a maido da dalibai da duk wadanda aka sace. Kuma Nijeriya ita ce daga karshe za tai nasara a kan ‘yan ta’adda da magoya bayansu na badinin da na bayyane.

 

Ko akwai wani karin bayani?

Yadda Amurka ta shiga kasar Viatenam ta kunyata, ta je Irak, Afghanistan da sauran kasashe ta kunyata, to haka za ta kunyata idan ta yi yunkurin shigowa Nijeriya. Bayin Allah na nan babu dare ba rana na addu’a, yara kanana na yi ,ga dabbobi, saboda haka in Allah ya yarda makiya Nijeriya ba su yi nasara ba. Nijeriya za ta yi nasara daga karrshe.

Kasashen Afirika muna da tarihi na turjiya ga mulkin mallaka da kasashen ‘yan mamaya, don haka kada wata kasa ta yi tunanin za ta zo tai mamu katsilandan tai nasara. Kwanan nan Nijar, Mali da Burkina Faso suka kori Turawa saboda sun kasa taimakon su kan matsalar tsaro, don haka ya kamata ‘yan kishin kasa mu farka, mu kuma shirya. Ba mu da wata kasa da ta wuce Nijeriya, kuma a shirye muke mu kare ta daga azzaluman kasashe masu tarihin cinikin bayi, mamaya da mulkin mallaka.

 

Mun gode

Nima na gode

Amurka
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba
Amurka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
  • Sulaiman
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • Sulaiman
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • Sulaiman
    An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

MASU ALAKA

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya
Rahotonni

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Rahotonni

Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa

July 11, 2026
Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
Next Post
Tawagar Shugaban Ƙasa Ta Isa Bauchi Don Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi

Tawagar Shugaban Ƙasa Ta Isa Bauchi Don Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.