Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta mayar da dukkanin motocin da ta kama daga hannun tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle zuwa kotu.
Wata tattaunawa ta wayar tarho da gidan Telebijin na Channels ya yi ranar Asabar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.
- ‘Yansanda Sun Kai Samame Gidan Matawalle, Sun Kwace Motoci 40
- Sakarci Da Talauci Ne Yasa Gwamnatin Zamfara Shiga Gidana Sata- Bello Matawalle
“Eh, rundunar ‘yan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkan motocin tsohon gwamna Bello Matawalle,” Cewar Kakakin ‘Yansandan.
“Mun mayar da dukkan motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya da ke Gusau, kamar yadda nake magana da ku yanzu, babu wata mota guda da ke hannun ‘yan sanda.”
A ranar 15 ga watan Yuni, mai shari’a Aliyu Bappa na babbar kotun tarayya Gusau ya umurci dukkanin jami’an tsaro da ke da ruwa da tsaki wajen kwashe motocin daga gidajen Matawalle na Gusau da Maradun da su dawo da su cikin sa’o’i 48.
Kotun ta kuma bayar da umarnin dakatar da wadanda ake kara a karar da Matawalle ya shigar a gaban kotu daga daukar wani mataki na gaba dangane da lamarin.
Wadanda suka amsa karar sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya da hukumar ‘yan sandan Nijeriya da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC).
Gidan Talabijin na Channels ya ziyarci babbar kotun tarayya da safiyar Lahadi domin tabbatar da wannan umarnin inda ya rawaito cewa motoci 29 ne kawai ke harabar kotun har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Sai dai majiyoyi sun ce har yanzu wasu motocin na nan a sansanin ‘yan sanda ana sa ran za su isa Gusau a yau Lahadi ko kuma safiyar Litinin.
Sai dai har yanzu tsohon gwamnan bai tabbatar da ko an dawo da motocin ba, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
A baya dai gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kwato fiye da motoci 40 da suka hada da motocin hana shigar harsashi guda uku da kuma SUV guda takwas daga gidajen tsohon gwamnan biyu.