Wata kotu a Jihar Kaduna ta umarci ‘yan sanda da su mayar wa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky, ababen hawansu da ake rike musu tun bayan takaddamar da ta barke tsakanin sojoji da almajiran malamin a Zariya shekara bakwai da ta wuce.
Da ya ke zanta wa da manema labarai a lokacin da ake mika motoci da babura, Barista M. Abu, lauyan da ke wakiltar ‘yan Shi’a, ya bayyana cewa da yawan motocin sun lalace.
- EFCC Ta Damke ‘Yan Damfarar Intanet 17 A Benue
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 2 A Jami’ar Zamfara
Ya ce, “Mun zo ofishin ‘yan sanda na MTD ne bisa hukuncin kotu da muka samu a madadin wadanda suka shigar da kara.
“Adadin ababen hawan da muka shigar da kara a kai ya kamata ya zarce adadin wadanda muka gani yanzu a nan. Ababen hawan da ke kasa a nan guda 67 ne kawai. Kuma ya kamata a ce sun fi haka. Ko wadanda muka gani a nan duk an lalata su. Bai kamata mu same su a wannan yanayin ba.
“Wadanda mafi yawa aka kwashe a gefen hanya da kuma gidan Malaminsu, Malam El-Zakzaky. Inda sojoji suka tattare musu ababen hawansu tare da kama mutane wanda suka mika wa rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su domin yanke musu hukunci.
“Amma a bangaren ababen hawansu wadanda aka ajiye a MTD, kuma ba a taba gabatar da su a gaban kotu ba a lokacin shari’a ba. Bayan wancan hukuncin mun dauki matakin ganin an bayar da ababen hawan amma hakan ya ci tura saboda wasu dalilai nasu dole ta sa muka shigar da kara kan hakan.”
Lauyan ya ce tun cikin shekarar 2022 kotun a karkashin mai shari’a A. A Amina ta bayar da umurin bayar da ababen hawan, “daga lokacin da kotun ta bayar da umarni zuwa yanzu ya dauki lokaci”, in ji shi.
Lauyan ya tabbatar da cewa za su duba matakin da za su dauka a gaba duba da cewa ababen hawan da aka ba su ba su kai wadanda suka shigar da kara suna nema ba.
Malam Sidi Muhammad Rabiu mazaunin garin Kaduna, ya ce; “Kayayyakin kamar yadda muka zo muka same su da yawansu an cire abubuwan da suke cikin babura da motoci, an cire injinansu. Mafi yawan kayayyakin sai dai ka dauki gwangwanin mota ko babur.”
Idan za a tuna dai biyo bayan faruwar lamarin na Zariya da ya wakana a watan Disamban 2015 daruruwan almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky ne suka rasa ransu sakamakon arangama da sojoji.
Lamarin ta kai ga tsare Zakzaky da matarsa da wasu mabiya na tsawon shekaru daga bisani aka sake su.