‘Yansanda a Kenya na tsare da ‘yan Kasar Habasha 24 da aka bari a wasu dazuka da ke lardin Isiolo a Arewa maso Gabashin kasar, kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.
An ce sun nemi agaji ne a wani ofishin ‘yansanda da ke yankin Merti bayan wadanda ake zarginsu da safarar su sun gudu sun bar su ranar Lahadi.
- Ya Kamata Manchester United Ta Kori Erik ten Hag?
- Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
An bayar da rahoton cewa, masu safarar mutanen da ba a san ko su waye ba sun gudu ne da niyyar kaucewa shingen bincike a kan babbar hanyar Isiolo zuwa Nairobi.
Bakin hauren sun shaida wa ‘yansanda cewa suna kan hanyar zuwa Afirka ta Kudu bayan sun tsallaka kan iyakar Kenya da Habasha.
‘Yan Habashan dai na hannun ‘yansanda suna jiran a gurfanar da su a gaban kuliya saboda kasancewarsu a kasar ba bisa ka’ida ba. ‘Yansanda sun ce za su ci gaba da neman masu safarar mutanen.
Kenya dai hanya ce ta gama-gari ga bakin hauren Habasha da ke yunkurin shiga Afirka ta Kudu.