Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Nasarawa.
Kakakin rundunar na babban birnin tarayya, Abuja, SP Josephine Adeh, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce, rundunar da hadin gwiwar sashen bayanan sirri sun kai hari maboyar ‘yan bindiga da ke kauyen Ukya ta Jihar Nasarawa da ke kan iyaka da babban birnin tarayya Abuja.
- Za Mu Dawo Da Martabar PDP A Katsina — Kwamitin Riƙon Ƙwarya
- Sanusi Ya Amince Da Mayar Da Wasu Ma’aikatun CBN Zuwa Legas
Rundunar ta yi artabu da maharan inda ta yi nasarar hallaka daya daga cikinsu.
“Jami’an ‘yansanda sun kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutane yayin da sauran suka tsere dajin da rauni.”
Ta ce rundunar ta ceto mutane 14 ba tare da sun ji rauni ba, sannan an sake hada su da ‘yan uwansu.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, CP Haruna Garba, ya jaddada kudirinsa na samar da zaman lafiya a birnin.
Kuma ya bukaci mazauna Abuja da kewaye da su ci gaba da ba da rahoton duk abin da ba su yarda da shi ba ta hanyar kiran wadannan lambobi: 08032003913, 08061581938, 07057337653, 08028940883 da kuma 09022222352.