Wani jirgin saman Max Air ya yi hatsari a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Lahadi sanadiyar fashewar tayar saukar jirgin wacce ta kama da wuta bayan saukar jirgin.
Wani jami’in kamfanin ya shaidawa LEADERSHIP cewa ba a samu asarar rai ba, domin an kwashe dukkan fasinjoji 144 da ma’aikatan jirgin 6 cikin koshin lafiya.
Jirgin dai ya taso ne daga Yola jihar Adamawa.
Hukumar ceto da kashe gobara (ARFFS) da ke aiki a filin jirgin ta yi gaggawar daukar matakin kashe gobarar.
Tsohon shugaban kungiyar likitocin Nijeriya (NMA), Dr. Mike Ogirima, wanda ya bada labarin faruwar lamarin ya ce tayar jirgin ce ta fashe tun a filin jirgin sama na Yola yayin tashin jirgin.
Don haka, jami’an kashe gobara da ke filin jirgin saman Abuja suk shirya tsaf suna jiran saukar jirgin.
Har yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya FAAN.