Sannan kuma wasu ma’aikatan sun gano yadda wasu ma’aikatan wadanda suke hada baki da Elizabeth da Balwani suke zuwa su samo sakamakon jinin da aka dauka na mutane a wasu guraren ta yadda ake yi wa mutane karya da yaudara cewa ai shi ne sakamakon.
Har ila yau masu bincike da dama sun nemi kamfanin Theranos da ya basu bayanai akan yadda Edison yake aiki ma’ana sirrin fasahar da suke amfani da ita wajen gano cutattukan da ke damun mutane, sai kamfanin ya ce ai wannan wani abu ne nasu na sirri wanda ba za su fada wa kowa ba saboda tsoron satar fasaha. Ta haka wannan kamfani ya yi ta yaudarar jama’a da jami’ai da kamfanoni yana basu sakamakon bogi.
- NDLEA Ta Kwace Kwaya Ta N1.5bn Da Cafke Mutum 1,078 Masu Safarar Kwaya A Kano.
- Dansanda Ya Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 1 Kan Ya Saki Wani Barawon Mutane A Kano
Duk wadancan bayanai Carriyou ya samosu ne ta wancan ma’aikacin wato jikan Henry Kessinger wanda ya ke a kamfanin a matsayin ma’aikaci. Shi kansa yace ba sau daya ba basau biyu ba ansha yi masa barazana saboda anga yadda yake wasu abubuwa a kamfanin.
Carriyou ya yanke shawarar rubuta wani abu a jaridar da yake yi wa aiki ta Wall Street Journal akan kamfanin na Theranos bayan binkicen da ya yi. Bayan wannan kamfani na Wall Street Journal sun wallafa labari akan kamfanin Theranos sai abubuwa suka fara fitowa fili. Jama’a da suke amfani da Edison suka yi ta rubutu a shafukan Twitter da sauran shafukan sada zumunta a game da yadda wannan na’ura ta kamfanin Theranos ta basu matsala. Kafin kamfanin Wall Street Journal su buga labarin Theranos sai da Elizabeth ta tsoratar da John Carriyou da kamfanin WSJ akan kada su kuskura su rubuta wani abu akan kamfaninta. Shi kuwa John maimakon ya yi sanyi wajen binkicen sai ya kuma azama domin samo gaskiyar lamari game da kamfanin da na’urar da yake sayarwa mutane.
A shekarar 2018 gwamnatin Amurka ta ba da umarnin dakatar da kamfanin daga aiki, sannan aka saka wasu kwararru su binciki wannan na’urar ta Edison, bayan binkicensu ya gano cewa Elizabeth Holmes karya kawai ta yi wa Amerikawa da masu zuba jari don ta sami kudi da za ta yi shagalinta ne. An gurfanar da su a gaban kotu a shekarar 2019 inda a wannan shekarar ta 2022 kotu ta same su da laifi, inda aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekara goma sha daya da watanni hudu.
Yanke mata hukuncin ke da wuya ta fadi a kasa tana gurshekan kuka inda da kanta ta bayyanawa duniya cewa hakika ta yi wa duniya karya, kuma ta dauka cewa wannan abin nata da ta kirkira zai yi aiki amma sai gashi abin ba haka bane. Sannan ta kara da cewa Ramesh Balwani shi ne ya cuce ta domin duk shi ne ya tsara yadda abin zai aiki a matsayinsa na masani akan harkar gwaje-gwajen lafiya.
Amma mai shari’ar ya amince a tsare Elizabeth a gidanta har ya zuwa watan Afrilun 2023 saboda tana da tsohon ciki, inda ya ce bayan ta haihu sai a mayar da ita kurkuku ta ci gaba da zaman hukuncin. Har ila yau za’a kwace dukkan dukiyarta da kudade domin biyan masu hannun jari da kuma mutanen da suka cutu saboda amfani da na’urar da suka yi.
Shima Ramesh Balwani an yanke masa nasa hukuncin zaman gidan kurkuku na shekaru 15, sannan zai mai do da kudi Dalar Amurka miliyan 804 don ba wa mutanen da suka zuba hannun jari a kamfanin.
Abin da ya sa na ba da wannan labarin na Elizabeth shi ne ta yadda jama’a za su koyi wani abu game da rikon amana da gaskiya wajen yin kasuwanci. Da farko dai Elizabeth tunaninta na wannan na’urar ta Edison mai kyau ne ta haka ne ya sa jama’a da yawa suka zuba jari a kamfanin har da shi dattijo Henry Kessinger.
Sannan mutane sun yarda cewa abin da ta fada Edison zai yi ana bukatarsa, saboda a wannan duniyar tamu gwajin jini ga marasa lafiya yana zamar musu aiki sosai saboda wani akan ce ya yi gwaji fiye da daya, amma sai gashi an zo da wata fasaha da mutum zai yi amfani da ita a digon jini sau daya inda za’a samu sakamako sama da 100.
Wannan ba karamin tunani bane da duniya za ta yi zumudin samunsa, amma sai dai kash ashe Elizabeth karya take yi wannan abin nata kwata-kwata ba wannan aikin yake yi ba, hasali ma a karshe zai nuna mutum yana da wata cuta wacce bama ya tunaninta.
Akwai wanda ya bayar da ba’asi a binciken inda bayan ya yi amfani da Edison sai sakamako ya nuna maganin da ya gama sha na HIB ya saka masa wata matsala a jikinsa.
A wannan lokacin yace to ai shi bai yi HIB ba lafiyarsa kalau, ya za’a yi ace ya sha maganin HIB kuma har ya saka masa wani abu a jikinsa? Nan da nan shima ya kai kara kuma duk irin wadannan bayanan aka tattara aka yi wa Elizabeth da farkanta hukunci a kotu. Da fatan wannan zai zama izina ga jama’a wajen kirkirar abin da ya ke gaskiya ba karya ba, domin duk abin da Allah ya tsaga rabonka ne zai same ka haka akasinsa.