Wata yarinya ‘yar shekara 13 mai suna Zuwaira Ahmed daga kauyen Kagara a Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, ta haddace tare da rubuta cikakken Alkur’ani mai girma.
Da ya ke jawabi a wajen bikin karrama yarinyar a yau Asabar, Hakimin Mahuta, Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba da aka samu.
- Mutane 20 Sun Kone Kurmus A Hatsarin Mota A Oyo
- Zan Yi Iyakar Kokarina Wajen Bunkasa Karamar Hukuma Garko A Jihar Kano -Salisu Musa Sarina
Ya bayyana cewa, wannan babbar nasara ce ga al’umma, da ma jihar baki daya, musamman a bangaren ilimin addinin Musulunci.
Abdulkadir, ya kuma yaba wa iyaye, malamai da sauran shugabannin al’umma kan yadda suke kula da tarbiyyar ‘ya’yansu yadda ya kamata, yana mai kira gare su da su ci gaba da yin hakan.
Danejin Katsina, ya bai wa sarakunan jihar tabbacin ci gaba da bada goyon baya ga duk wani abu da ya shafi addinin musulunci, domin ci gaban yankin baki daya.
Shugaban karamar hukumar Kafur, Garba Kanya, ya yaba da kwazon yarinyar tare da bada tabbacin tallafa mata a matakin karatunta na sakandire da manyan makarantu.
Shugaban makarantar ta, Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, ya ce an kafa makarantar ne da nufin yin tasiri na ingantaccen ilimin addinin Musulunci a tsakanin matasa a cikin al’umma.
A cewarsa, yarinyar ta haddace Alkur’ani ne a cikin shekaru hudu, kuma ya danganta nasarar da ta samu ga goyon bayan iyayenta da jajircewar malamanta a makaranta.
A nasa jawabin, mahaifin hafizar, Ahmed Sani, ya yaba da duk tallafin da aka ba shi da ‘yarsa, inda ya yi kira ga iyaye da su bar ‘ya’yansu su samu ilimin addinin musulunci da na boko.
Ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba ta goyon bayan da ya dace don kuma ta ci gaba da karatun ta na boko, inda ya ce a halin yanzu tana makarantar firamare a yankin.